A karshe, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Ya ce Ya Tsaya da Ƙafarsa

A karshe, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Ya ce Ya Tsaya da Ƙafarsa

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce ya tsaya da ƙafarsa yayin da shugabannin yan kwadago suka ziyarce shi
  • Abba Kabir Yusuf ya ce ba yadda za a yi shugaba ya yi yaki da cin hanci da rashawa ba tare da ya tsaya da kafafunsa ba
  • Gwamnan ya ce da ba a kan ƙafarsa yake tsaye ba, ba za a ga yana gudanar da ayyukan cigaba a sassan jihar Kano ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi magana da ke ishara da martani ce ga masu kiran 'Abba tsaya da ƙafarka.'

Gwamnan ya bayyana cewa dama a kan ƙafarsa yake tsaye kuma ayyukan da yake yi a jihar Kano sun tabbatar da haka.

Kara karanta wannan

Kudirin haraji: Sanata Ali Ndume ya yi barazanar ficewa daga jam'iyyar APC

Abba Kabir
Abba Kabir ya ce ya tsaya da kafarsa. Hoto: Sanusi Bature Dawakin Tofa
Asali: Facebook

Daraktan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ne ya wallafa bayanan da gwamnan ya yi a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba ya ce ya tsaya da ƙafarsa a Kano

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa na yaki da cin hanci da rashawa ba sani ba sabo.

Gwamnan ya ce hakan na nuni da cewa yana tsaye ne a kan ƙafarsa domin in ba haka ba. da labarin ya canza.

Ga jawabin gwamnan da Sanusi Bature ya wallafa:

"Idan ba ina tsaye a kan kafata ba, da ba zan iya yin ayyukan cigaba da ake gani a jihar Kano ba.
Duk shugaban da zai saka kafar wando da cin hanci da rashawa, dole ya tsaya da ƙafarsa. Kuma a kan kafata na ke tsaye."

- Abba Kabir Yusuf

'Karin albashi babban abu ne' inji Abba

Abba Kabir Yusuf ya ce karin albashi babban lamari ne a jihar musamman idan aka lura da kuɗin da Kano ke samu a wata.

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna Uba Sani ya karbi kasurguman yan bindiga da suka tuba

Gwamnan ya ce bayan an yi karin albashi, jihar Kano za ta rika kashe karin Naira biliyan shida domin biyan ma'aikata.

Abba Kabir Yusuf ya kuma bayyana cewa a mako mai zuwa zai ziyarci wasu daliban da jihar Kano ta tura Indiya karatu.

Abba zai tura dalibai karatu jami'o'i

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf ta fara kara shirin tura ƴaƴan talakawa karatu jami'oi.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamiti mai dauke da mutane 18 da zai tantance daliban da za a zaba kafin a tura su karatun.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng