'Ya Fi Bala'in Cire Tallafi: Sheikh Salihu Zaria Ya Yi Tofin Allah Tsine kan Kudirin Haraji
- Yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan sabon kudirin haraji, Sheikh Abubakar Salihu Zaria ya nuna damuwa kan halin da ake ciki
- Shehin malamin ya kira sunan wasu yan siyasa inda ya yi musu addu'o'in bala'i yayin da ya yabawa Sanata Ali Ndume
- Wannan na zuwa ne bayan sabon kudirin haraji ta tsallake karatu na biyu a Majalisar Tarayya ana tsaka da halin kunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Sheikh Abubakar Salihu Zaria ya fusata kan maganar sabon kudirin haraji a Najeriya.
Shehin malamin ya caccaki dukan sanatoci da sauran yan siyasa da ke goyon bayan kakaba harajin a kasar.
Sheikh Salihu Zaria ya magantu kan dokar haraji
Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na TikTok a yau Juma'a 29 ga watan Nuwambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Salihu ya ce bala'in da za a shiga kan wannan haraji sai ya fi halin da aka shiga dalilin cire tallafin mai.
Shehin ya ce abin takaici ne yadda wasu sanatoci har da Sanata Barau Jibrin ke goyon bayan dokar.
"Kun san maganar harajin nan an tura majalisa, kuma wadannan azzaluman suna shirin sanya hannu ciki har da Barau Jibrin, ya Allah wanda ya sanya hannu a wannan haraji domin ya ci zabe, Ubangiji yasa ya rasa ta da wacce ya ke nema, ya rusa jin dadin kudin da ya tara."
"Duk dan Majalisar da ke goyon bayan wannan haraji munafiki ne, wanda ya kirkiro harajin ma munafiki ne, duk wanda yake da hannu a wannan haraji da neman saka mu a bala'i sai mun kira sunansa mun roka masa bala'i."
"Hatsarin wannan haraji ya fi fitinar cire tallafin mai, fitinar da za mu shiga Allah ne kadai zai fitar da mu, yan siyasa sun yaudare mu, ruwa babu shi, wuta babu ita, hanyoyi babu su da sauran bangarori."
- Sheikh Salihu Abubakar Zaria
Malamin ya yabawa Sanata Ali Ndume kan kokarinsa inda ya caccaki Sanata Barau da cewa Allah ya yi maganinsa.
Dokar haraji ta tsallake karatu na 2
Kun ji cewa Majalisar Dattawa ta amince kudirorin sake fasalin haraji sun tsallake karatu na biyu a zaman jiya Alhamis, 28 ga watan Nuwambar 2024.
Sanatoci sun yi muhawara kan kudirin bayan jawabin shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele.
Asali: Legit.ng