Ma'aikata Za Su Warwasa, Gwamnan Osun Zai Fara Biyan Sabon Albashin N75,000
- Gwamnatin jihar Osun karkashin jagorancin Gwamna Ademola Adeleke ta ce za ta fara biyan sabon mafi karancin albashi a watan Disamba
- Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Kolapo Alimi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a, 29 ga watan Nuwamba
- Tun farko dai Gwamna Adeleke ya amince da N75,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi a jihar Osun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Osun - Gwamnatin jihar Osun za ta fara biyan sabon mafi karancin albashi na N75,000 ga ma’aikatan gwamnati a ranar 1 ga Disamba, 2024.
Gwamnatin ta bayyana cewa za ta haɗawa ma'aikatan da bashin wata ɗaya da suka biyo idan aka fara biyan sabon albashin.
Gwamnan Osun zai fara biyan albashin N75,000
A wata sanarwa da ta wallafa a shafin X, gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne a wani taro da aka gudanar a karkashin jagorancin mataimakin gwamnan Osun, Kola Adewusi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron ya samu halartar manyan ƙusoshin gwamnatin Osun da wakilan ƴan kwadago ƙarƙashin jagorancin shugaban NLC na jihar, Kwamared Chris Arapasopo.
Gwamnatin Osun za ta biya bashin wata ɗaya
Da yake jawabi bayan taron, kwamishinan yaɗa labarai, Kolapo Alimi ya ce:
"Za mu fara biyan mafi karancin albashi na N75,000 a ranar 1 ga Disamba, 2024, kuma za mu biya bashin wata daya.”
“Wannan wani bangare ne na kudirin gwamnatin Gwamna Ademola Adeleke na inganta jin dadi da walwalar ma’aikata a jihar Osun."
Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnatin Adeleke ta nuna dagaske take yayin da ta zarce adadin N70,000 da gwamnatin tarayya ta amince da shi.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyar NLC ta sake jaddada cewa za ta fara yajin aiki a jihohin da suka gaza fara biyan sabon albashin daga ranar 1 ga watan Disamba.
Gwamnan Kaduna ya fara biyan N72,000
Rahoto ya gabata cewa gwamnatin Uba Sani ta fara aiwatar da sabon mafi karancin albashin N72,000 da ta yiwa ma'aikatan Kaduna alkawari a Oktoba.
Sanarwa daga babban mataimaki ga Gwamna Uba Sani kan sababbin kafofin sadarwa, ta ce an fara biyan kudin daga Nuwamba.
Asali: Legit.ng