Gwamnatin Kano Ta Sauya Magana, Ta Fadi Mamallakin Shinkafar 'Tinubu' da Aka Kama

Gwamnatin Kano Ta Sauya Magana, Ta Fadi Mamallakin Shinkafar 'Tinubu' da Aka Kama

  • Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ta karyata kanta kan kama shinkafar tallafin gwamnati
  • Hukumar a karkashin Barista Muhyi Magaji Rimingado ta gano buhunan shinkafa 16,800 da ake sauyawa buhu dauke da hoton Tinubu
  • Da fari, an yi zargin tallafin gwamnatin tarayya da aka bayar a watan azumin da ya gabata ne, amma yanzu akwai sabon bayanai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC) ta janye maganar da ta yi a baya kan buhun shinkafa 16,800 da ake zargin na tallafin Tinubu ne.

Shugaban hukumar, Barista Muhyi Magaji Rimingado ya yi karin bayani kan aininin mamallakin shinkafa da aka yi zargin an karkatar da ita tun da fari.

Kara karanta wannan

Zargin almundahana: Bayan EFCC ta dafe shi, kotu ta yarda a tsare Yahaya Bello

Tinubu
PCACC ta ce shinkafar Tinubu ba ta tallafi ba ce Hoto: Shehu Yako Yako
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Barista Muhyi Magaji ya bayyana cewa an kawo shinkafar ne daga Bauchi da Zamfara, amma ba tallafin gwamnatin tarayya ba ce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su wanene suka mallaki ‘shinkafar Tinubu’?

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ta bayyana cewa wani bawan Allah mai taimakon jama’a ya mallaki shinkafa sama da buhu 16,000 da aka kama da hoton Bola Tinubu.

“Na wani mutum ne mai taimakon jama’a wanda ya samar da shinkafar kuma yake rarraba ta ga jama'a don tallafawa siyasar Shugaban Ƙasa.

‘Ba shinkafar Tinubu ba ce,’ gwamnatin Kano

Muhuyi Magaji Rimingado ya kara da cewa mutanen da aka kama a shagon ma’aikata ne da bawan Allah da ya Sakaye sunansa ya dauka don kula da aikin tallafinsa.

Shugaban PCACC ya gode wa al’ummar jihar Kano tare da ƙarfafa su da su ci gaba da bayar da muhimman bayanai ga hukumar don yaƙar cin hanci da sauran laifuka a jihar.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan Kogi ya musanta zargin almundahanar N110bn da EFCC ke yi masa

An kama buhunan shinkafa da hoton Tinubu

A wani labarin, kun ji yadda hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC) ta kai samame unguwar Hotoro, inda aka kama wani shago makare da buhunan shinkafa.

An gano buhuna guda biyu, daya mara rubutu, daya kuma dauke da hoton Tinubu, inda aka rubuta cewa 'ba ta sayarwa ba', lamarin da ya sa aka rika zargin ta tallafin gwamnati ce.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.