Shugaba Tinubu Ya Fadi Abin da Ya Kamata Najeriya ta Koya wajen Faransa
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa akwai kyakkyawar alaka tsakanin Najeriya da Faransa
- Shugaban ya bayyana haka ne a daren Alhamis, lokacin liyafar cin abinci da gwamnatin Faransa ta shirya a Paris
- Bola Ahmed Tinubu ya ce gwagwarmayar da Faransa ta shiga kafin ta kawo matakin da ta ke a yanzu, abin koyi ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar France - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jinjina wa dangantaka mai karfi tsakanin Najeriya da Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macro.
Bola Tinubu ya bayyana kwarin gwiwar cewa dangantakar da aka samar a tsakanin kasashen biyu zai amfanar da nahiyar Afrika baki dayanta.
Wannan na kunshe a cikin sanarwar da hadimin shugaban kasar kan kafafen yada labarai, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X a ranar Juma’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya nemi kara inganta alaka da Faransa
Hadimin shugaban kasa, Sunday Dare ya wallafa shafinsa na X cewa shugaba Tinubu ya nemi yan Najeriya da na kasar Faransa da su cigaba da kyautata alaka a tsakaninsu.
Ya mika bukatar hakan a lokacin liyafar cin abinci ta gwamnatin Faransa da aka shirya wa shugaba Tinubu a Palais des Elysée a Paris a daren Alhamis.
Bola Tinubu zai yi koyi da Faransa
Shugaban kasar Najeriya ya bayyana yadda Faransa ta burge shi ta fuskokin cigaba har ta kawo matakin da ta ke a yanzu.
Bola Ahmed Tinubu ya ce;
“Faransa ta sha wahala kafin ta cimma ‘yanci, dimokuradiyya, kuma wannan abin koyi ne a gare mu.”
Shugaban ya yaba da yadda Faransa ta bude kofar kasuwanci ga 'yan Afrika kamar su Alhaji Aliko Dangote, AIG Imoukhuede da Tony Elumelu.
Bola Ahmed Tinubu bayyana cewa nan gaba akwai kyakkyawar dama don kyautata alaƙar Najeriya da Faransa.
Shugaba Tinubu ya sauka a Faransa
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasar nan, Bola Tinubu da mai dakinsa, Sanata Remi Tinubu sun isa Faransa bisa gayyatar shugaban kasar, Emmanuel Macron domin ziyarar aiki.
Shugaban, wanda ya samu cikakkiyar karramawa daka dakarun Faransa, ya sauka a filin jirgin sama na Orly da misalin karfe 5:10 na yammacin ranar Laraba agogon Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng