Cire Tallafi: Tinubu Ya Samar da Motocin Gas domin Zirga Zirga Kyauta a Najeriya

Cire Tallafi: Tinubu Ya Samar da Motocin Gas domin Zirga Zirga Kyauta a Najeriya

  • Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da motoci masu amfani da gas domin samar da saukin zirga-zirga a birnin Abuja
  • Gwamnatin ta ware motoci har 15 saboda zirga-zirgar mutane kyauta daga yanzu har zuwa watan Janairun 2024
  • Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin ta cire tallafin mai da take ganin ya jefa al'umma cikin wani irin hali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Domin ragewa yan Najeriya radadin cire tallafi, Gwamnatin Tarayya ta samar da motoci domin zirga-zirgar mutane kyauta.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da samar motocin bas masu amfani da gas domin zirga-zirgar mutane kyauta a Abuja.

Tinubu ya samar da motoci kyauta domin zirga-zirgar al'umma a Najeriya
Gwamnatin Bola Tinubu ta kaddamar da motoci kyauta da za a yi zirga-zirga a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, @PBATmediacenter.
Asali: Facebook

Bola Tinubu ya ba da motocin zirga-zirga kyauta

Shugaba Tinubu ya kaddamar da motocin ne a jiya Alhamis 28 ga watan Nuwambar 2024, kamar yadda BusinessDay ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Majalisa ta sa ranar taron kasa, za a zauna kan batun haraji, kananan hukumomi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin ta mika motoci guda 15 ga kungiyoyin sufuri da ke Abuja a kokarin tabbatar da inganta rayuwar al'umma.

Mazauna birnin Abuja za su ci gajiyar amfani da motocin kyauta daga yanzu har zuwa 6 ga watan Janairun 2024.

Ministan sufuri ya shawarci yan Najeriya

Ministan sufuri, Sanata Sa'idu Alkali ya tabbatar da cewa hakan na daga cikin tsarin gwamnatin Tinubu na 'Renewed Hope' a kasar.

Sanata Alkali ya ce hakan zai taimaka wurin ragewa al'umma halin kunci da suka shiga dalilin cire tallafin mai a kasar, cewar The Guardian.

Ministan ya bukaci yan Najeriya su karbi shirin hannu bibbiyu tare da nuna goyon baya ga gwamnati domin inganta rayuwarsu.

Rahotanni sun tabbatar da cewa motocin za su bi sanannun wurare kamar Mararaba da Eagle Square da tashar mota ta Berger da sauransu.

Gwamna ya ware motoci kyauta domin zirga-zirga

Kun ji cewa gwamnatin jihar Edo ta samar da bas kyauta a fadin jihar domin yin zirga-zirgar al'ummarta kyauta.

Kara karanta wannan

Kudirin Haraji: Sheikh Mansur Sokoto ya ba 'yan majalisa shawara ana zargin maƙarƙashiya

Gwamna Monday Okpebholo shi ya amince da hakan domin saukakawa al'umma duba da halin kunci da ake ciki.

A cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar, an ji matakin zai shafi dukan mazabun Tarayyan jihar da cikin birnin Benin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.