Gwamnatin Tinubu Ta Dauki Wasu Matakai 2 na Kawo Karshen Yajin Aikin Ƴan Kwadago

Gwamnatin Tinubu Ta Dauki Wasu Matakai 2 na Kawo Karshen Yajin Aikin Ƴan Kwadago

  • Ministan kwadago, Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi, ya ce gwamnati ta dauki matakan hana ma'aikata shiga yajin aiki
  • Alhaji Maigari Dingyadi, ya kara da cewa ba da ilimi da horaswa ga ma'aikata zai taimaka wajen rage yawaitar yajin aiki
  • Ministan ya bayyana hakan ne a wani taron bita da aka shiyarwa kungiyoyin kwadago, inda aka tattauna batutuwa da dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ministan kwadago da ayyuka na Najeriya, Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi, ya ce gwamnati za ta kawo karshen yajin aikin 'yan kwadago.

Ya jaddada muhimmancin kafa kwararrun ma'aikata da za su rage yawan shiga yajin aiki a wuraren ayyukansu wanda ke jawo tasgaro ga ci gaban kasa.

Ministan kwadago ya yi magan kan magance yajin aikin ma'aikata a Najeriya
Gwamnatin tarayya ta bayyana matakan kawo karshen yajin aikin ma'aikata a Najeriya. Hoto: @LabourMinNG, @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

Hanyoyin magance yajin aiki a Najeriya

Alhaji Dingyadi ya bayyana haka ne a wajen taron bita na kungiyoyin kwadago karo na 7 da aka gudanar a Abuja ranar Laraba inji rahoton Arise News.

Kara karanta wannan

Yakubu Gowon: Abin da yake ci mani tuwo a kwarya game da matsalar Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya bayyana cewa ma’aikatarsa tana kokarin hana yajin aiki ta hanyar tattaunawa da ma'aikatan da aka batawa rai da tabbatar da an biya su hakkokinsu.

Ya bukaci ma'aikatun gwamnati da na 'yan kasuwa da su rika tattaunawa da ma’aikata, su saurari koke-koken su, sannan su bayar da mafita don guje wa yajin aiki.

Ana taron horar da 'yan kwadago

Alhaji Dingyadi ya jaddada muhimmancin ilimi da ba da horo ga ma'aikara, inda ya ce wani mataki ne na rage barkewar yajin aiki a kai a kai da kuma inganta aiki.

Ya bayyana batutuwan da za a tattauna a taron da suka hada bitar halaccin shiga yajin aiki, hakkokin ma’aikata da kuma muhimmancin tattaunawar kai tsaye.

Sauran batutuwan sun hada da yadda za a gudanar da al'amuran kungiyoyin kwadago da kuma kalubalen da ake fuskanta game da aiwatar da sabon albashin N70,000.

Kara karanta wannan

Jigawa ta yi zarra tsakanin jihohi, ta yi wa ma'aikata gata bayan ƙarin albashi

'Yan kwadago za su shiga yajin aiki

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyoyin kwadago, NLC da TUC na shirin tsunduma yajin aiki a wasu jihohi hudu saboda kin fara biyan sabon albashin N70,000.

Kungiyoyin kwadago sun sanya ranar 1 ga watan Disamba a matsayin wa'adin da dukkanin jihohi za su fara biyan mafi ƙarancin albashi ko su shiga yajin aikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.