Majalisa Ta Sa Ranar Taron Kasa, Za a Zauna kan Batun Haraji da Kananan Hukumomi

Majalisa Ta Sa Ranar Taron Kasa, Za a Zauna kan Batun Haraji da Kananan Hukumomi

  • Majalisar wakilan Najeriya za ta zauna da jama'a domin jin ra'ayinsu a kan muhimman batutuwa da su ka shafi kasa
  • Kwamitin da ke duba kundin tsarin mulkin Najeriya da yadda za a yi masa kwaskwarima ne zai jagoranci zaman
  • Za a tattauna da shiyyoyin kasar nan shida domin jin ra'ayinsu kan yancin kananan hukumomi da sauye-sauyen haraji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Kwamitin Majalisar Wakilai kan sake duba Kundin Tsarin Mulkin kasa na 1999, ya sanar da shirinsa na gudanar da tattaunawa ta kasa kan muhimman batutuwa.

Kwamitin ya ce za a tattauna kan 'yancin kan kananan hukumomi, wacce kotun ƙolin ƙasar nan ta tabbatar masu a shekarar 2024.

Kara karanta wannan

An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hezbollah

Majalisa
Kwamitin majalisar wakilai za ta yi babban taron kasa Hoto: House of Representatives
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa mataimakin kakakin majalisar wakilai kuma Shugaban Kwamitin, Benjamin Okezie Kalu ne ya sanar da haka a zaurensu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa za ta zauna kan 'yancin kananan hukumomi

Shugaban kwamitin duba kan kundin tsarin mulkin, Benjamin Onesie Kalu 1999 ya ce za a gudanar da taron a ranar 2 Disamba, 2024.

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa majalisa za ta zauna don tattaro ra’ayoyi da dabarun inganta ‘yancin kan kananan hukumomi a Najeriya

'Yan Majalisar tarayya za su duba batun haraji

Kwamitin majalisar wakilan kasar nan zai zauna da jama’a don tattaunawa kan sauye-sauyen haraji da suka shafi gyaran kundin tsarin mulki. Kwamitin ya kuma ce ya na shirin fara sauraren ra’ayoyin jama’a a matakin shiyya a watan Janairu na shekarar 2025.

Majalisa na shirin taron shiyyoyin kasa

Za a gudanar da wannan sauraron ra’ayoyi a jihohi 12 da ke wakiltar shiyyoyi Arewa ta Gabas, Arewa maso Tsakiya, Arewa maso Yamma, Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu da Kudu maso Yamma.

Kara karanta wannan

Yan majalisa za su gwabza kan bukatar Tinubu na cin bashin $2.2bn

Jihohin da aka zaba don sauraron ra’ayoyin sun hada da Gombe da Borno, Nasarawa da Neja, Kaduna da Sakkwato, Enugu da Imo, Bayelsa da Cross River da Legas da Ondo.

An fafata kan tsarin haraji a majalisa

A wani labarin, kun ji cewa an samu muhawara mai zafi a majalisar dattawa kan kudurin harajin da shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya aika domin a sahale masa.

Yan majalisa irinsu Abdul Ningi da Ali Ndume sun ja daga, suna ganin rashin dacewar kasar nan ta nemi ɗorawa jama'a haraji, saboda halin kunci da aka jefa su tun da fari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.