Dokar Haraji: Sanatocin Arewa Sun Yi Ganawar Sirri bayan Kudirin Ya Tsallake Karatu na 2

Dokar Haraji: Sanatocin Arewa Sun Yi Ganawar Sirri bayan Kudirin Ya Tsallake Karatu na 2

  • Sanatocin Arewa sun gudanar da taron sirri a ranar Alhamis bayan kudurin dokar gyaran hajraji ya tsallake karatu na biyu
  • Sai dai ba a gano abin da ganawar ta kunsa ba, yayin da shugaban kungiyar, Sanata Abdulaziz Yar'Adua ya ki cewa komai
  • Dokokin harajin da shugaba Bola Tinubu ya gabatar da suka hada da dokar kafa hukumar NRS sun jawo ce-ce-ku-ce mai zafi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Sanatocin Arewa sun yi wata ganawar sirri a ranar Alhamis bayan kudurin dokar sake fasalin haraji ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar dattawa.

Legit Hausa ta rahoto cewa dokar sake fasalin haraji da shugaba Bola Tinubu ya gabatar na ci gaba da shan suka, inda dattawan Arewa suka nuna adawa da ita.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi abin da ya kamata Najeriya ta koya wajen Faransa

Sanatocin Arewa sun yi wata ganawar sirri yayin da kudurin dokar gyaran haraji ya wuce karatu na biyu.
Sanatocin Arewa sun saka labule kan kudurin dokar sake fasalin haraji. Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

Sanatocin Arewa sun gana kan dokar haraji

Jaridar Punch ta rahoto cewa sanatocin Arewa sun gudanar da taron ne a dakin taro na 301 da ke zauren majalisar, kuma sun shafe kimanin awanni biyu a ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, ba a bayyana cikakken bayani game da tattaunawar ba, domin shugaban kungiyar Sanatocin Arewa, Sanata Abdulaziz Yar'Adua, ya ki yin magana a kai.

Sai dai ana tunanin tattaunawar ba za ta rasa nasaba da yadda gwamnoni, sarakunan gargajiya, dattawa da masu ruwa da tsaki a Arewa ke adawa da dokar harajin ba.

Majalisa za ta saurari ra'ayoyi kan dokar haraji

A ranar Alhamis, majalisar ta umurci kwamitin kudi na majalisar ya gayyaci gwamnoni, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki don jin ra'ayinsu kan dokar.

Kafin wannan ne aka ce 'yan majalisar sun shiga ganawar sirri domin tattauna batutuwan dokar a sirrance.

Bayan dawowarsu daga ganawar ne shugaban masu rinjaye, Opeyemi Bamidele (APC, Ekiti Tsakiyar), ya jagoranci muhawara kan dokokin.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta tafka muhawara, kudirin harajin Tinubu ya tsallake karatu na 2

Tinubu ya gabatar da dokar gyaran hari

A wani labarin, mun ruwaito cewa a watan Oktoba, shugaba Bola Tinubu ya tura dokoki hudu na haraji zuwa majalisar tarayya don duba su.

Dokokin sake fasalin harajin sun hada da dokar kafa hukumar kula da kudin shiga ta Najeriya (2024), dokar kafa hukumar NRS da sauransu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.