"Ba Yanzu ba:" Sanata Ndume Ya Fadi Lokacin da Ya Dace a Bijiro da Kudurin Haraji
- Sanata Ali Ndume ya bayyana dalilin da ya sa har yanzu ya ke cigaba da adawa da manufar gwamnatin tarayya kan haraji
- Sanatan da ke wakiltar Borno ta Kudu ya ce wannan ba lokaci ne da ya dace a bullowa da 'yan Najeriya karin kudin haraji ba
- Ya ce akwai lokacin da ya dace gwamnati ta kawowa jama'a dokar karin haraji ba tare da an nuna rashin jin dadin hakan ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume ya bayyana dalilansa na kin goyon bayan kudurin harajin gwamnatin tarayya.
A ranar Laraba ne Sanatan ya ja daga da mataimakin shugaban majalisa, Barau I Jibrin wajen nuna kiyayya ga kudirin canza tsarin haraji.
A hira da ya yi da Channels Television, Sanata Ali Ndume ya ce na da ka ya ke kin kudurin da zai kara dorawa yan Najeriya haraji ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin Ali Ndume na kin kudurin harajin Tinubu
Sanata Ali Ndume ya shaida cewa lokacin da gwamnatin Najeriya ta zaba na kakaba dokar haraji, sam bai dace ba.
Ya ce Najeriya kasa ce da ke fama da matsaloli da yawa, daga cikinsu akwai yunwa da rashin abin hannu a wajen jama'a.
Sanata Ndume ya fadi lokacin da ya dace a kara haraji
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa 'yan Arewa ba cima zaune ba ne, sun dade su na biyan haraji tun iyaye da kakanni ba tare da wasu matsaloli ba.
Ya kara da cewa ba biyan haraji ake gudu ba, amma kamata gwamnati ya yi ta jira sai mutane su na iya cin abinci su koshi, da biyan sauran bukatunsu kafin neman karin haraji.
Ndume ya ja daga game da kudurin haraji
A wani labarin, kun ji cewa Sanatan Borno, Ali Ndume ya fafata da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I Jibrin a kan kudurin harajin da shugaba Bola Tinubu ya aike masu.
Duk da kin amincewar wasu daga cikin 'yan majalisa, an gayyata shugabannin FIRS da DMO kan batun, lamarin da Sanata Abdul Ningi da Ali Ndume su ka ce ya sabawa dokar majalisa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng