Ma'aikata Gwamnati Na cikin Alheri Dumu Dumu, Gwamna Ya Fara Biyan Albashin N72000

Ma'aikata Gwamnati Na cikin Alheri Dumu Dumu, Gwamna Ya Fara Biyan Albashin N72000

  • Gwamnatin Uba Sani ta fara aiwatar da sabon mafi karancin albashin N72,000 da ta yiwa ma'aikatan Kaduna alkawari a Oktoba
  • Sanarwa daga babban mataimaki ga Gwamna Uba Sani kan sababbin kafofin sadarwa, ta ce an fara biyan kudin daga Nuwamba
  • Gwamnatin jihar ta bukaci ma'aikatan Kaduna da su hanzarta kai koke ofishin babban akawun jihar idan sun ga gibi a albashin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Gwamnatin Kaduna karkashin Malam Uba Sani ta cika alkawari na fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan jihar.

Legit Hausa ta rahoto cewa Gwamna Uba Sani, ya amince da mafi karancin albashi na N72,000 ga ma’aikatan jihar, daga watan Nuwamba 2024.

Gwamnatin jihar Kaduna ta aika sako ga ma'aikata yayin da ta fara biyan N72,000
Gwamnatin Kaduna ta fara biyan sabon mafi karancin albashi na N72,000. Hoto: @Abdool85
Asali: Twitter

An fara biyan albashin N72,000 a jihar Kaduna

Abdallah Yunus Abdallah, babban mataimaki na musamman (sababbin kafafen sadarwa) ga Uba Sani ne ya sanar da fara biyan albashin a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Jigawa ta yi zarra tsakanin jihohi, ta yi wa ma'aikata gata bayan ƙarin albashi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar Abdullahi ta yi nuni da cewa ofishin babban akawun jihar ya fara biyan sabon mafi karancin albashin na N70,000 kamar yadda Gwamna Uba Sani ya umarta.

Gwamnatin jihar ta yi kira ga ma'aikata da su kai korafi ga sashen karbar korafe korafe na ofishin babban akawun jihar idan sun samu kasa da N72,000.

Gwamnatin Kaduna ta aika sako ga ma'aikata

Cikakkiyar sanarwar na cewa:

"Ofishin Akanta Janar ya yi nasarar aiwatar da umarnin Gwamna Uba Sani game da biyan sabon mafi karancin albashi na N72,000 na watan Nuwamba 2024.
"Don Allah, kar ayi jinkirin gabatar da koke ga sashen korafi da bincike na ofishin babban akawun jihar Kaduna idan kun ga wata shaidar biyan kuɗi na ƙasa da N72,000."

Karanta sanarwar a nan kasa:

Gwamna Abba ya fara biyan sabon albashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta fara biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N71,000.

Kara karanta wannan

Gwamna ya rikita ma'aikata da farin ciki, sun fara jin karbar albashin N85,000

Wannan dai na zuwa makonni uku bayan Gwamna Abba ya karɓa kuma ya amince da rahoton kwamitin albashi da ya kafa kan sabon mafi karancin albashin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.