'Tsohon Mai aka Saka a Matatar Fatakwal,' An Zargi NNPCL da Rufa Rufa

'Tsohon Mai aka Saka a Matatar Fatakwal,' An Zargi NNPCL da Rufa Rufa

  • An zargi kamfanin man Nigeria na NNPCL da ɓoye gaskiya kam hakikanin halin da matatar man Najeriya da ke Fatakwal ke ciki
  • Wani mazaunin yankin da matatar ke aiki, Timothy Mgbere ya ce akwai abubuwan da gwamnati bata fada daidai ba a kan matatar
  • Hakan na zuwa ne yayin da kamfanin NNPCL ya sanar da cewa an fara tace mai a matatar bayan shafe shekaru baya aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Kungiyar mazauna yankin Alesa da matatar Fatakwal ke aiki ta ce akwai lauje cikin naɗi kan buɗe matatar da aka ce an yi.

Sakataren kungiyar, Timothy Mgbere ya ce maganar cewa matatar ta dawo aiki ba da kyau gaskiya ba ne.

Matata
An zargi gwamnati da boye gaskiya kan matatar Fatakwal. Hoto: NNPC Limited
Asali: Twitter

Timothy Mgbere ya bayyana haka ne a cikin wata hira da ya yi da Arise TV a yau Alhamis, 28 ga Nuwamba.

Kara karanta wannan

Bayan gyara matatar Fatakwal, kamfanin Dangote ya fara tallan man fetur

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matatar Fatakwal ta fara aiki?

Sakataren kungiyar cigaban yankin da matatar Fatakwal ke aiki ya zargi gwamnati da boye gaskiya kan gyaran matatar.

Timothy Mgbere ya ce matatar ba ta fara aiki kamar yadda ake fada ba, kuma cewa motoci 200 za su cigaba da ɗaukar mai a Fatakwal ba gaskiya ba ne.

Punch ta wallafa cewa Mgbere ya yi zargin cewa man da aka ce an tace ma tsoho ne da ya dade a wajen.

"Abin da aka nuna na cewa matatar Fatakwal ta fara aiki ya yi kama da damfara. Har yanzu ba ta wani aikin a zo a gani.
Bana so na furta cewa sun yi karya amma bai kamata NNPCL ya fadawa yan Najeriya zancen da ba gaskiya ba.
Man da suka ce sun tace tsoho ne, ya kai shekaru uku a wajen. Matatar ba ta tace mai lita miliyan 1.4 kamar yadda suka faɗa."

- Timothy Mgbere

Kara karanta wannan

IPMAN: 'Yan kasuwa sun fadi abin da zai kawo cikas ga samun saukin farashin fetur

Mista Mgbere ya ce motoci shida aka loda daga tsohon man da ke matatar amma kuma NNPCL ya ce za su rika loda motoci 200.

A karshe, Timothy Mgbere ya ce ba lallai yan Najeriya su yarda da abin da ya fada ba, amma dai shi ya gama na shi.

Ana hasashen saukin farashin mai

A wani rahoton, kun ji cewa dillalan mai sun nuna farin ciki da fara dakon mai da NNPCL ya yi daga matatar Fatakwal bayan gyarata.

IPMAN da MEMAN sun bayyana cewa kara wadatar man fetur zai haifar da gasa, wanda a karshe zai rage farashin fetur a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng