Yan Bindiga Sun Kashe Tsoho Mai Shekaru 85 bayan Karɓar Kudin Fansa
- Rahotanni na nuni da cewa wani tsohon mai shekaru 85 a jihar Filato ya hadu sharrin 'yan bindiga masu garkuwa da mutane
- An ruwaito cewa masu garkuwa da mutane sun kama Deh Idi Dakum ne a ranar 18 ga watan Nuwamba da misalin karfe 7:00 na dare
- 'Yan bindigar da suka kama dattijon sun bukaci kudin fansa a wajen iyalansa kuma an biya su kudin kafin a gano sun kashe shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Filato - 'Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sace wani dattijo mai shekaru 85, Deh Idi Dakum a jihar Filato.
Rahotanni na nuni da cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Matelem a karamar hukumar Bokkos ta jihar Filato.
Premium Times ta wallafa cewa Deh Idi Dakum ya kasance shi ne Galadiman Nyam a masarautar Tangur.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kashe dattijo mai shekaru 85 a Filato
Tun a ranar 18 ga Nuwamba da 'yan bindiga suka sace Deh Idi Dakum ba a samu damar magana da masu garkuwa ba sai ranar 19 ga wata.
Dan gidan marigayin, Bala Dakum ya zantawa kamfanin dillancin labarai na NAN cewa miyagun sun yi amfani da wayar mahaifiyarsu da suka sace ne wajen kiransu.
Bayan 'yan bindigar sun bukaci kudin fansa, iyalan marigayin sun tura musu a ranar 20 ga watan Nuwamba.
"Bayan biyan kudin fansa suka ce za su sake shi domin a cewarsu yana wani waje tare da manyansu.
Haka muka ta jira har ranar 23 ga wata, da muka kira su sai suka ce kudin ya yi kadan kuma daga nan muka fara tunanin akwai matsala.
A safiyar ranar 23 ga wata da misalin karfe 9:00 na safe aka samu gawar mahaifinmu a cikin wata gona. Sun kashe shi!"
- Bala Dakum
Shugaban karamar hukumar Bokkos da sarkin Matelem na cikin waɗanda suka halarci jana'izar Deh Idi Dakum.
Bala Dakum ya bayyana cewa 'yan bindiga na shawagi a kauyen Matelem a ko da yaushe, babu mai hana su.
An kama masu taimakon yan bindiga
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sanda a jihar Bauchi ta kama wasu mutane da ake zargi da cewa suna hada kai da yan bindiga wajen garkuwa da mutane.
Ana zargi matasan da tara bayanan mutanen da ke zaune a gari musamman baƙi su mika ga miyagu domin a yi garkuwa da su saboda kudi.
Asali: Legit.ng