IBB, Tambuwul da Manyan Mutanen da ke Fuskantar Barazanar Rasa Filaye a Abuja

IBB, Tambuwul da Manyan Mutanen da ke Fuskantar Barazanar Rasa Filaye a Abuja

  • Hukumar lura da birnin tarayya, Abuja (FCTA) ta wallafa sunayen waɗanda ake bin bashin kudin fili a wurare daban daban
  • Tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida na cikin waɗanda aka wallafa sunayensu saboda bashi
  • Rahotanni na nuni da cewa hukumar FCTA ta sanyawa mutanen wa'adin biyan bashin kudin ko kuma su fuskanci barazana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar lura da birnin tarayya Abuja ta yi barazana ga mutane 9,532 da ba su gama biyan kudin filaye ba.

Tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida da wasu tsofaffin gwamnoni na cikin waɗanda FCTA ke bi bashi.

Babangida
Manyan Najeriya da ke fuskantar barazanar kwace filaye a Abuja. Hoto: Anas Manga
Asali: Twitter

Rahoton the Cable ya nuna cewa mutanen da aka biyo bashin za su iya rasa filayensu idan ba su biya kudin ba a kan lokaci.

Kara karanta wannan

"Mun Haramta Hayaniya," Gwamnatin Legas ta rufe babban wurin ibada da wasu otel

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan da aka biyo bashin fili a Abuja

1. Ibrahim Babangida

Tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida na cikin mutanen da hukumar FCTA ke bin bashin kudin fili a Abuja.

Ana bin IBB bashin kudi har Naira miliyan 152 a kan wani katafaren fili da ya mallaka a unguwar Asokoro a babban birnin.

2. Samuel Ortom

Tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom na cikin waɗanda aka biyo bashin kudin fili a birnin tarayya Abuja.

Ana bin Samuel Ortom bashin N950,000 a kan wani fili da ya mallaka a unguwar Bazango da ke Abuja.

3. Aminu Tambuwal

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal na cikin manyan da hukumar FCTA ta biyo bashi.

Daily Post ta wallafa cewa FCTA na bin Sanata Tambuwal bashin Naira miliyan 18 a kan filin da ya mallaka a Carraway Dallas.

Sauran waɗanda ake bi bashin a Abuja

Rundunar yan sanda, sojojin ruwan Najeriya, gwamnatocin Legas da Kaduna na cikin wadanda ake bi bashin.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya tsoratar da Tinubu, ana zargin EFCC ta fara bincike domin karya shi

FCTA ta ba su wa'adin mako biyu su kammala biyan kudin ko kuma su fuskanci barazanar kwace mallakar filayen.

An hana kwace filin Bello Matawalle

A wani rahoton, mun ruwaito muku cewa wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta hana kwace filaye shida na tsohon gwamnan jihar Zamfara dake Abuja.

Rahotanni su nuna cewa alkalin kotun ya amince ta matsayar lauyan Bello Matawalle na cewa kotu ba ta da wannan hurumin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng