Yakubu Gowon: Abin da Yake Ci Mani Tuwo a Kwarya game da Matsalar Arewa
- Tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon ya bayyana fargaba kan yadda shiyyar Arewa ke fuskantar gagarumar matsalar tsaro
- Ya shaida abin da yake ci masa tuwo a kwarya lokacin da tawagar tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau ta kai masa ziyara
- Tsohon shugaban ya ce akwai hanyar da yankin Arewa za ta bi wajen kakkabe matsalolin da ke zama barazana a gare ta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Plateau - Tsohon Shugaban Kasa, Yakubu Gowon, ya bayyana lamarin Arewacin kasar nan da ke sanya shi a cikin damuwa.
Ya fadi damuwarsa a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar tafiyar siyasa da tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya kafa.
A wani rahoto da ya kebanta da Channels Televsion, tsohin Shugaban Kasar ya ce yadda rashin tsaro ke kara dabaibaye shiyyar, abin damuwa ne matuka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yakubu Gowon ya fadi damuwarsa game da Arewa
Tsohon shugaban Najeriya, Yakubu Gowon ya yi takaicin yadda rashin tsaro ya yi kamari, har aka samu bullar sabuwar kungiyar 'yan ta'addan Lakurawa.
Ya ce abubuwa marasa dadi da ke faruwa a kasar nan, musamman a shiyyar Arewa su na bukatar a kawo karshensu.
Janar Gowon kasa ya fadi fatansa kan Arewa
Janar Yakubu Gowon mai ritaya ya bayyana yadda Arewacin Najeriya za ta iya kawo karshen kalubalen da su ka sako ta a gaba.
Ya ce;
"Duk da bambanci da ke tsakaninmu, idan za mu iya hada kai ta hanyar kawar da sabanin da mu ke da su, za mu kawo karshen matsalolin da mu ke fuskanta."
Ya kuma yaba da yadda tafiyar Malam Ibrahim Shekarau ta ga dacewar kai masa ziyara, inda ya ce hakan mutunta shi ne ainun.
Gwamna Kaduna ya nemi taimakon Tinubu
A baya mun ruwaito cewa gwamnan Kaduna, Uba Sani ya sanar da Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu irin mawuyacin halin da yan ta'adda su ka sanya jama'a a sassan jiharsa.
Ya shaidawa shugaban halin da mutane ke ciki ne a lokaci da ya ziyarce shi a fadar gwamnati, duk da dai a cewarsa, an samu wasu nasarori da dama a yaki da ta'addanci a Kaduna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng