Hukumar Kwastam Za Ta Karya Farashin Man Fetur na Wasu Kwanaki
- Hukumar kwastam ta kama man fetur mai tarin yawa da aka nufi fita da shi daga Najeriya da haramtacciyar hanya a Taraba da Adamawa
- Kakakin hukumar ya bayyana cewa za su sayar da man fetur din ga yan Najeriya a farashi mai rahusa domin rage radadin rayuwa
- A bayanin da hukumar ta yi, ta ce an kama mafi yawan man fetur din ne a jarakuna da durom yayin da ake shirin fita Kamaru da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Adamawa - Hukumar kwastam za ta yi gwanjon man fetur da ta kama a jihohin Adamawa da Taraba.
Jami'an Operation Whirlwind ne suka kama man fetur din ana shirin fita da shi kasashen waje ta barauniyar hanya.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa hukumar kwastam ta ce kama fetur din zai rage tsada da wahalar mai da ake fama da su a yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwastam za ta rage kudin fetur
Hukumar kwatsam ta kama man fetur da ya haura lita 71,965 ana shirin shiga da shi kasashen ketare.
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa hukumar kwastam ta ce kudin fetur din da aka kama ya haura Naira miliyan 81.5.
Shugaban Operation hukumar kwastam na kasa, Adewale Adeniyi ya umarci a sayar da man fetur din da araha a birnin Yola na jihar Adamawa.
An kama masu safarar man fetur a Adamawa
Shugaban Operation Whirlwind na kasa, Hussain Ejibunu ya ce a yanzu haka an kama masu safarar man zuwa ƙetare.
Hussain Ejibunu ya tabbatar da cewa ana binciken waɗanda aka kama domin musu hukunci.
Jami'an Kwastam sun nemi hadin kan jami'ai
Shugaban hukumar kwastam a jihohin Adamawa da Yola, Garba Bashir ya buƙaci jami'an tsaro su rika hada kai.
Garba Bashir ya ce yaki da safarar man fetur a iyakoki na bukatar hadin kan dukkan jami'an tsaro domin samun nasara.
Kwastam ta kama fetur a Neja
A wani labarin, mun ruwaito muku cewa hukumar kwastam ta kasa ta bayyana gagarumin aikin da ta ke na dakile safarar man fetur zuwa kasashen ketare.
Kwastam ta kama masu kokarin fasa kwaurin man fetur da ya kai lita 67,000 a iyakar Neja da Kwara ana kokarin fitar da shi waje.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng