Bayan Gyara Matatar Fatakwal, Kamfanin Dangote Ya Fara Tallan Man Fetur
- Tallan fetur da matatar Dangote ta fara ya ja hankalin jama'a, inda wasu ke ganin kishiyar da aka yi a Fatakwal ne sila
- Kamfanin Dangote ya wallafa tallan fetur din da ya ke fitarwa ne shafukansa, haka kuma an hango allon tallan a titi
- Matatar ta fara daukar matakin kiran kasuwa ne kasa da mako biyu da kammala gyaran matatar mai ta Fatakwal
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos - Kwanaki kadan da gyara matatar mai ta Fatakwal, an hango matatar Dangote da ke Legas ta fara tallata fetur da ta ke tacewa.
An hango allo dauke da tallan fetur din Dangote, inda aka yi kira ga abokan ciniki su sayi man fetur mai inganci daga matatar.
A sakon da matatar ta wallafa a shafin X, ta ce fetur din da aka sarrafa a cikinta da cewa ya na da kyau ga motoci, injuna, da kuma muhalli.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matatar Dangote ta na tallan fetur
Jaridar The Cable ta wallafa cewa matatar Dangote ta shaidawa yan Najeriya cewa ta rage farashin litar fetur zuwa N970, ta bukaci jama’a su rika sayen fetur din da ta ke sarrafawa.
Sakon da aka wallafa a shafin Dangote Group ya ce;
“Ku sayi akalla lita miliyan 2 a kan N970 kowace lita.”
Wannan ne karo na farko da akasarin 'yan Najeriya ke ganin ana tallan man fetur, ganin yadda ake rububinsa wajen amfanin yau da kullum.
Dangote: Martanin ‘yan Najeriya kan tallan fetur
Wasu daga cikin ‘yan kasar nan a shafin X sun rika martani ga yadda matatar Dangote ta fara tallata man fetur; duk da wasu na ganin abu ne mai kyau, wasu sun mayar da shi zolaya.
@ChrisimehJ ya ce;
“#400 albarka”.
@EmodiMba ya wallafa cewa;
“Alhaji, mai zai hana a fara samar da fetur dan leda, za a yi ciniki sosai.”
@CeeZamila ya ce;
“Wannan abu ne mai kyau. Ina rokon masu gidajen mai su rika saye daga Dangote kai tsaye su rage farashin zuwa N970.”
"Tataccen man Dangote na N20,000 ba zai kai motoci biyu mako biyu ba."
Matatar Dangote ta rage farashin fetur
A wani labarin kun ji cewa matatar mai ta Dangote da ke Legas ta bayyana rage farashin litar fetur da ta ke sayarwa dillalan mai zuwa kasa da N990 da ta sanar a watan Nuwamba.
Matatar ta rage farashin kowace lita daga N990 da ta sanar baya zuwa N970, wanda hakan zai ba yan kasuwa damar samun rara ta N20 a kan kowace lita idan a hada da tsohon farashi.
Asali: Legit.ng