Jigawa Ta yi Zarra Tsakanin Jihohi, Ta yi wa Ma'aikata Gata bayan Ƙarin Albashi

Jigawa Ta yi Zarra Tsakanin Jihohi, Ta yi wa Ma'aikata Gata bayan Ƙarin Albashi

  • Gwamnatin jihar Jigawa karkashin jagorancin Malam Umar A. Namadi ta sanar da ƙarin mafi ƙarancin albashin ma'aikata
  • Umar Namadi ya bayyana cewa Jigawa ta zamo ta daban a tsakanin jihohin Najeriya saboda gatan da ta yi wa ma'aikatanta
  • Leggit ta tattauna da wata malamar makaranta a jihar Jigawa domin jin ko abubuwan da gwamnan ya lissafa sun fara iso su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana tsare tsaren da ta yi domin tallafawa ma'aikata.

Hakan na zuwa ne bayan gwamna Umar A. Namadi ya ayyana N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.

Namadi
An karawa ma'aikata albashi a Jigawa. Hoto: Garba Muhammad
Asali: Twitter

Legit ta tatttaro bayanan da gwamnatin ta yi ne a cikin sokon da hadimin gwamna Namadi, Garba Muhammad ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Abba ka cika gwarzo: Ma'aikata sun yabawa gwamnan Kano bayan dafe sabon albashi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi wa ma'aikata gata a jihar Jigawa

Gwamnatin jihar Jigawa ta fitar da tsarin da zai kawo sauƙin rayuwa ga ma'aikata bayan shiga tsadar rayuwa a Najeriya.

Bayan kyautatawa dukkan ma'aikata, jami'an lafiya za su samu gata kamar yadda ake yi wa ma'aikatan gwamnatin tarayya.

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa gwamnatin za ta rika sayar da abinci da araha ga ma'aikata tare da ba su bashi.

"Duk da cewa mun ayyana N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, fa'idar da za a samu a Jigawa ta haura N80,000.
A jihar Jigawa ne kawai ma'aikata suke da shagon da ake sayar musu da abinci a farashi mai rahusa kuma ake ba su bashi.
A Jigawa ne kawai za a rika ba manoma bashi domin su rika noma abin da za su ci a cikin shekara."

Ma'aikata sun yabi gwamnatin Jigawa

Gwamna Umar Namadi ya ce ma'aikatan jihar za su huta da fargabar tashin farashi idan suka noma abin da za su ci.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya cika alkawari, ma'aikata sun fara cin sabon albashin N71,000

Shugaban kungiyar kwadago, Sanusi Alhassan Maigatari ya yabawa gwamna Umar Namadi bisa daura jihar a turba mai kyau.

Legit ta tattauna da malamar makaranta

Wata malamar makaranta a Jigawa, Ikilima Adamu ta zantawa Legit cewa za su yi farinciki da abubuwan da gwamnan ya lissafa zai musu.

Ikilima ta bayyana kasancewar a yanzu ne aka fara maganar, suna fata abin zai tabbata kuma za su samu damar cin gajiyarsa.

An fara biyan sabon albashi a Rivers

A wani rahoton, kun ji cewa ma'aikata a jihar Rivers sun cika da farin ciki bayan Gwamna Siminalayi Fubara ya fara biyan mafi karancin albashi.

Gwamna Siminalayi Fubara ya biya daukacin ma'aikatan jihar mafi karancin albashin akalla N85,000 kamar yadda ya yi alkawari a baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng