Babban Jagora a NNPP Ya Fice daga Jam'iyyar, Ya Zayyano Dalilansa
- Jam'iyyar adawa ta NNPP a jihar Oyo ta rasa ɗaya daga cikin manyan jagororinta wanda ya ke kan gaba wajen samar mata da kuɗi
- Alhaji Adebisi Olopoeyan wanda jagoran NNPP ne a yankin Kudu maso Yamma ya sanar da fucewarsa daga jam'iyya mai kayan dadi
- Ya bayyana cewa ya yi amanna matakin da ya ɗauka shi ne abin da ya dace duk da gudunmawar da ya ba da wajen gina jam'iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Oyo - Jagoran NNPP na yankin Kudu maso Yamma, Alhaji Adebisi Olopoeyan ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar.
Alhaji Adebisi Olopoeyan, wanda ya kasance jagaron NNPP a yankin Kudu maso Yamma, shi ne ke kan gaba wajen samar da kuɗi ga jam'iyyar a jihar Oyo.
Jagoran NNPP ya fice daga jam'iyyar
Tsohon jagoran na NNPP ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alhaji Adebisi wanda tsohon jigon PDP ne a jihar Oyo ya koma jam'iyyar NNPP sama da shekaru biyu da suka gabata.
Meyasa Adebisi Olopoeyan ya fice daga NNPP?
Tsohon jigon na NNPP ya bayyana cewa ya yi murabus daga jam'iyyar ne bisa wasu dalilai na ƙashin kansa, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
Ya bayyana cewa lokaci ya yi da zai bar jam'iyyar, duk da irin gudunmawar da ya ba da wajen ginuwarta tun bayan shigowarsa a shekarar 2022.
Alhaji Adebisi ya kuma nuna godiyarsa ga shugaban kwamitin amintattu na ƙasa na jam'iyyar, Boniface Aniebonam da sauran shugabanninta, kan irin ƙaunar da suka nuna masa lokacin da yake tare da su.
"Duba da abubuwan da suke faruwa, ya zama tilas na yi murabus daga jam'iyyar NNPP nan take. Yayin da wannan mataki ne mai wahalar ɗauka, na yi amanna cewa shi ne wanda ya dace."
- Alhaji Adebisi Olopoeyan
PDP ta dakatar da ɗan majalisar dokoki
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar PDP a Bauchi ta dakatar da ɗaya daga cikin ƴa ƴanta a majalisar dokokin jihar.
Jam'iyyar PDP ta dakatar da ɗan majalisar da ke wakiltar ƙaramar hukumar Kirfi, Habibu Umar, saboda zargin rashin biyayya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng