'Yan Kasuwa Sun Fadi Farashin da NNPCL Ya Sayar Masu da Man Fetur

'Yan Kasuwa Sun Fadi Farashin da NNPCL Ya Sayar Masu da Man Fetur

  • Kungiyar Petroleum Products Retail Outlet Owners Association of Nigeria ta musanta rahoton cewa an kara farashin fetur
  • Shugaban PETROAN na kasa, Dakta Billy Sotubo ya bayyana cewa kamfanin NNPCL ya sayar masu fetur a tsohon farashi
  • Sai dai dillalan na ganin za a samu saukin farashi, yayin da su ke jiran kamfanin mai na kasa ya fadi sabon kudin mai a yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Btayanai sun zo cewa kungiyar nan ta PETROAN ta dillan man fetur ta fadi gaskiyarta kan batun karin farashin litar man fetur.

Wannan na zuwa ne bayan wani kusa a kungiyar ya ce kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya kara masu farashi bayan gyara matatar Fatakwal.

Kara karanta wannan

IPMAN: 'Yan kasuwa sun fadi abin da zai kawo cikas ga samun saukin farashin fetur

fetur
PETROAN ta ce ba a kara mata farashin fetur ba Hoto: NNPC Limited
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa shugaban PETROAN na kasa, Dakta Billy Sotubo Gillis-Harry ya karyata cewa NNPCL ya kara masu kudin mai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda NNPCL ya sayar da man fetur

Jaridar The Sun ta wallafa cewa kungiyar masu kasuwancin man fetur karkashin inuwar PETROAN ta tabbatar da cewa NNPCL ta sayar masu da fetur bisa tsohon farashi.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, Dakta Gillis-Harry ya ce;

“PETROAN na farin cikin fara samar da mai a matatar Fatakwal, kuma muna jiran sabon farashi da NNPC zai sanar.”

Ana jiran sabon farashin fetur daga NNPCL

Kungiyar PETRON ta bayyana cewa duk da ‘ya’yanta na jiran kamfanin NNPCL ya shaida masu sabon farashin da zai rika sayar masu da fetur.

Shugaban kungiyar ya bayyana cewa su na fatan sabon farashin da NNPCL zai bayyana zai yi wa yan Najeriya dadi.

Yan kasuwa na hasashen farashin NNPCL

A wani labarin kun ji cewa dillalan man fetur a kasa, kamar su IPMAN da MEMAN sun fara hasashen saukowar farashin litar mai bayan kammala gyaran matatar Fatakwal.

Kara karanta wannan

An yanke farashin fetur a matatar Fatakwal, man NNPCL ya fi na Dangote tsada

Yan kasuwar na ganin karin matata da aka samu a cikin Najeriya zai haddasa gasa, wanda hakan zai taka rawa a kan farashin da ake sayarwa da jama'a litar fetur a gidajen mai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.