Jerin Kasashe 7 da ba a Biyan Haraji yayin da Ake Surutun Sabon Kudirin Haraji a Najeriya

Jerin Kasashe 7 da ba a Biyan Haraji yayin da Ake Surutun Sabon Kudirin Haraji a Najeriya

A ƴan kwanakin nan ƴan Najeriya na ci gaba ce-ce-ku-ce kan sabon tsarin harajin VAT wanda shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya tura majalisar dattawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Dokar harajin ta harzuka mutane musamman ƴan Arewa duba da halin matsi da wahalar da al'aumma ke ciki tun bayan tuge tallafin man fetur.

Bola Tinubu da shugaban kwamitin haraji na shugaban kasa.
Jerin wasu kasashe da mutane ba su biyan haraji Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Kudurin haraji ya harzuka ƴan Arewa

Gwamnonin jihohin Arewa sun nuna rashin gamsuwa da sabuwar dokar harajin bisa abin da suka kira da rashin adalci da daidaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai duk da haka, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya jaddaɗa cewa ba gudu ba ja da baya a yuƙurinsa a sauya fasalin tsarin haraji.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafin X, mai ba shugaban shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya ce Tinubu ba zai janye kudirin ba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa cikin asibiti, sun yi awon gaba da ƙwararren likita a Najeriya

Jerin kasashen da ba a biyan haraji

Sakamakon haka ne Legit Hausa ta binciko maku wasu ƙasashen duniya da al'ummar ƙasar ba su biyan ko kwandala da sunan haraji.

Akwai ƙasashe da dama waɗanda ke da tattalin arziƙin, kuma gwamnatin ƙasahen ba su jiran sai mutane sun biya haraji kafin gudanar da al'amura.

Waɗannan ƙasashe suna da daɗin zama kuma sun shahara wajen ƙin biyan haraji, ga su kamar haka:

1. Kasar Bahamas

Bahamas na ɗaya daga cikin shahararrun wuraren yawon buɗe ido a duniya, kuma a kasar mutane ba su biyan harajin kuɗaɗen shigar da suke samu.

Ƙasar ta ɗaukewa mutane biyan haraji kuɗin shiga ne domin jawo hankalin masu zuba jari musamman attajirai da ke bukatar samun shaidar zama a Bahamas

Sai dai duk da haka Bahamas na da tsarin biyan harajin VAT da kuma harajin kadarori, in ji rahoton Bussiness day.

2. Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE)

Haɗaɗɗiyar daular Larabawa watau UAE tana da ƙarfin tattalin arziki fiye da sauran ƙasashen gabas ta tsakiya, ƴan kasar ba su biyan harajin kudin da suke samu.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan ya gano matsalar da ta hana Najeriya samun cigaba

Wannan ya sa manyan birane a kasar kamar Dubai da Abu Dhabi suka yi fice, suka zama manyan mutane da ƙwararru na sha'awar zama a cikinsu.

Ƙasar UAE tana samun maƙudan kudin shiga daga albarkatun mai, don haka mazauna ke rayuwarsu ba tare da biyan haraji ba.

Amma kamfanonin mai da bankunan ƙasashen waje suna biyan harajin VAT a kan mafi akasarin kayayyaki da ayyukan da suke yi.

3. Kasar Qatar

Ƙasar da ke da arzikin iskar gas, Qatar tana bai wa al'ummarta damarmaki da dama wanda ya haɗa da ɗauke harajin kuɗin shiga.

Sai dai kasar tana kakaba haraji kan masana'antu da kamfanonin kasahen ketare kamar dai UAE, rahoton jaridar Times of India.

4. Monaco

Monaco birni ne mai zaman kansa a yankin Riviera na Faransa wanda ya kai girman ƙasar Vatican sau biyar, mutane ba su biyan haraji a birnin, rahoto ya tabbatar.

An gina manya-manya kuma ƙayatattun tashohin jiragen ruwa waɗanda ke jan hankalin mutanenn duniya.

Duk da Monaco na ɗaya daga cikin birane mafi tsadar zama, yana ɗaya daga cikin wuraren da ke da ƙarancin aikata laifuka.

Kara karanta wannan

Abia: Dakarun sojoji sun far wa ƴan Bindiga, an fara musayar wuta mai zafi

5. Bermuda

Bermuda wani yanki ne na Birtaniyya a Arewacin Tekun Atlantika wanda ke da rairayi a bakin teku mai ban sha'awa da ƙayatarwa.

Gwamnati ba ta sanya haraji a kan jama'arta amma dai akwai tsadar rayuwa, sai dai tsarin na rashin ƙaƙabawa kowa haraji na jan hankalin 'yan kasashen waje da kamfanoni.

Bermuda ta fi kyau da haɓaka fiye da Caribbean, yankin yana da ingantattun tituna da harkokin sufuri. Mutanen kasar ba su wuce 64,000.

6. Vanuatu

Tsibirin Vanuatu wata kayatacciyar ƙasa ce da ke cikin Tekun Pasifik, kuma ba ta karɓar harajin kuɗin shiga, harajin dukiya, ko harajin riba daga jama'arta.

Wuri ne da ya shahara kuma duk waɗanda ke neman salon rayuwa mai sauƙi da arha, mara haraji kamar masu ritaya da masu karbar fansho to can ne ya dace da su.

7. Cayman Islands

Kamar yadda Vanguard ta rahoto, mutanen tsibirin Cayman Islands ba su biyan kowane irin haraji, babu harajin VAT, harajin dukiya da dai sauransu.

Kara karanta wannan

NLC ta ba Gwamna Radda wa'adi kan shiga yajin aiki a Katsina

Gwamnati na samun kudaden shiga ta hanyar harkokin kasuwanci, kudaden izinin aiki, da harajin bangaren hada-hadar kudi.

Waɗannan ƙasashen  galibi wuraren yawon buɗe ido ne da ke jan hankalin masu neman zuba hannun jari a ƙasa, babu haraji amma akwai muhalli mai kyau.

Kudirin harajin Tinubu ya shiga karatu na 2

A wani rahoton, kun ji cewa Majalisar Dattawa ta amince kudirorin sake fasalin haraji sun tsallake karatu na biyu a zaman yau Alhamis, 28 ga watan Nuwamba

Sanatoci sun yi muhawara kan kudirin bayan jawabin shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262