Ciroman Kano: Aminu Sanusi II Ya Kai Ziyarar Farko Jigawa, Ya Gana da Gwamna
- Bayan nada Aminu Muhammadu Sanusi II a matsayin Ciroman Kano, basaraken ya yi wata ziyara ta musamman jihar Jigawa
- Ciroman Kano, DSP Aminu Muhammadu Sanusi II ya gana da gwamnan Jigawa da sarkin Dutse a yau Laraba, 27 ga Nuwamba
- Aminu Sanusi II ya samu rakiyar manyan mutanen fada da suka hada da Dokajin Kano, Dan Darman da Sarkin Yakin Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Jigawa - Jihar Jigawa ta karbi baƙuncin sabon Ciroman Kano, DSP Aminu Muhammadu Sanusi II.
DSP Aminu Sanusi II ya gana da gwamna Umar Namadi da mai martaba sarkin Dutse, Hamim Nuhu Muhammad Sanusi.
Hadimin gwamna Umar A. Namadi a bangaren yada labarai, Garba Muhammad ya wallafa hotunan ziyarar a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aminu Sanusi II ya ziyarci gwamna Namadi
Sabon Ciroman Kano, Aminu Muhammadu Sanusi ya gana da gwamna Umar A. Namadi yayin da ya ziyarci jihar Jigawa.
Jami'an gwamnati da suka hada da mataimakin gwamnan Jigawa, Aminu Usman Gumel ne suka karbi tawagar basaraken a Dutse.
Wannan ita ce ziyara ta farko da Aminu Muhammadu Sanusi II ya yi zuwa jihar Jigawa tun bayan nada shi matsayin Ciroman Kano.
Ciroma Aminu Sanusi II ya ziyarci sarkin Dutse
Bayan ganawa da gwamna Umar A. Namadi, Aminu Muhammadu Sanusi II ya ziyarci masarautar Dutse.
Mai girma Ciroman Kano ya gana da mai martaba sarkin Dutse, Hamim Nuhu Muhammad Sanusi a fadarsa da ke Garu.
An ruwaito cewa Aminu Sanusi II ya samu rakiyar Dokajin Kano, Sarkin Yakin Kano, Wamban Ringim da sauran manyan ƴan fada.
Kano: Abba ya nemi hadin kan sarakuna
A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya bayyana muhimmancin sarakunan gargajiya game da tsare-tsaren gwamnatinsa.
Gwamnan ya bukaci goyon baya daga sarakunan gargajiya duba da yadda suke kusa da al'umma wurin wayar musu da kai.
Hakan na zuwa ne yayin da hadimin gwamnan a bangaren masarautu ya kai ziyara ta musamman a fadar mai martaba Sarkin Rano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng