Zargin Almundahana: Bayan EFCC Ta Dafe Shi, Kotu Ta Yarda a Tsare Yahaya Bello

Zargin Almundahana: Bayan EFCC Ta Dafe Shi, Kotu Ta Yarda a Tsare Yahaya Bello

  • Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi zaman farko domin yanke hukunci a shari'ar da EFCC ke yi da Yahaya Bello
  • Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati na zargin tsohon gwamnan Kogi da wasoso da kudin jama'a
  • Ana zarginsa da wasu mutun biyu da sace N110bn da mallakar kadarori a babban birnin tarayya Abuja ta haramtacciyar hanya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Babbar kotun tarayya ta fara sauraron karar da hukumar yaki da yi wa kasa ta’annati (EFCC) ta gabatar gabanta kan zargin tsohon gwamna, Yahaya Bello da almundahana.

Hukumar EFCC ta na zargin tsohon gwamnan da karkatar da Naira biliyon 80 na mutanen Kogi zuwa aljihunsa domin biyan bukatar kashin kai.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan Kogi ya musanta zargin almundahanar N110bn da EFCC ke yi masa

Yahaya Bello
Kotu ta aika Yahaya Bello kurkuku Hoto: @tboss_guy
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa Mai Shari’a Maryanne Anenih ta bayar da umarnin a mika Yahaya Bello hannun EFCC ta cigaba da tsare shi zuwa ranar da za a cigaba da sauraron shari’ar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta aika Yahaya Bello hannun EFCC

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Mai Shari’a Maryanne Anenih ta umarci EFCC ta cigaba da ajiyar Yahaya Bello har ranar 10 Disamba, 2024.

Ana zargin tsohon gwamnan da wasu mutum biyu, Shuaibu Oricha da Abdulsalam Hudu da laifuffuka 16 na handame kudin talakawan jihar Kogi.

Kotu za ta saurari bukatar Yahaya Bello

Babbar kotun tarayya ta ce za ta saurari bukatar Yahaya Bello na bayar shi beli bayan nasarar gurfanar da shi a gabanta da hukumar EFCC ta yi.

An jima ana kai ruwa rana tsakanin EFCC da tsohon gwamnan wanda aka rika nema ruwa a jallo bayan kin mutunta gayyatar da hukumar ta yi masa, da bijirewa gurfana a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi a gaban kotu a Abuja

Yahaya Bello ya musanta zargin EFCC

A wani labarin, kun ji yadda tsohon gwamnan Kogi ya bayyana a gaban babbar kotun tarayya da ke Maitama a Abuja domin fara fuskantar shari’a da hukumar EFCC kan almundahana.

Yahaya Bello ya karyata zargin da EFCC ta ke yi masa na cewa ya wawashe kudin mutanen da ya mulka da yake ofis a Lokoja.

An ji cewa ana kuma tuhumar tsohon gwamnan da mallakar kadarori ta haramtacciyar hanya a babban birnin tarayya, Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.