An Yanke Farashin Fetur a Matatar Fatakwal, Man NNPCL Ya Fi na Dangote Tsada

An Yanke Farashin Fetur a Matatar Fatakwal, Man NNPCL Ya Fi na Dangote Tsada

  • Kungiyar masu harkar man fetur ta kasa (PETROAN) ta yi magana kan farashin litar mai a matatar man gwamnati ta Fatakwal
  • PETROAN ta bayyana cewa akwai bambancin farashi kadan a tsakanin matatar man Najeriya ta Fatakwal da matatar Dangote
  • Kakakin kungiyar PETROAN ya ce shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari ya yi alkawarin daidaita farashin matatun man

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Yayin da ake tsammanin samun sauki, kungiyar yan kasuwar man fetur ta bayyana sabon farashin litar mai a matatar Fatakwal.

Kakakin kungiyar, Dr Joseph Obele ya ce akwai bambancin N75 tsakanin matatar Dangote da ta Fatakwal.

Fatakwal
Man matar Fatakwal ya fi na Dangote tsada. Hoto: NNPCL Limited
Asali: Twitter

Rahoton Channels Television ya nuna cewa akwai yiwuwar kamfanin NNPCL ya rage farashin mai a matatar Fatakwal.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farashin man fetur a matatar Fatakwal

Kara karanta wannan

Matatar Fatakwal: Ƴan kasuwa sun hango farashin da fetur zai iya komawa a Najeriya

Daily Post ta wallafa cewa kungiyar yan kasuwar man fetur ta PETROAN ta ce matatar man Fatakwal za ta rika sayar da lita a kan N1,045.

Kakakin kungiyar, Dr Joseph Obele ne ya bayyana haka yayin bikin fara tace mai a matatar Fatakwal a ranar Talata.

Farashi a matatar Fatakwal da ta Dangote

Kungiyar PETROAN ta ce a halin yanzu, matatar Dangote tana sayar da litar man fetur a kan N970 a Najeriya.

Hakan na nuni da cewa man fetur a matatar Dangote ya fi sauki da N75 duk da cewa matatar Fatakwal mallakar gwamnati ce.

Tun bayan fara tace mai a matatar Fatakwal yan Najeriya suka kasa kunne domin jin yadda farashin man fetur zai kasance.

NNPCL za ta daidaita farashin fetur

Kakakin PETROAN, Dr Joseph Obele ya ce shugaban NNPCL, Mele Kyari ya yi alkawarin daidaita farashin mai a matatar Fatakwal da ta Dangote.

Dr Joseph Obele ya ce Kyari ya yi alkawarin ne domin kawo sauki ga yan kasuwa da masu amfani da man fetur a Najeriya.

Kara karanta wannan

Gyaran matatu: Tinubu ya yabi Buhari, za a gyara matatar da ke Arewacin Najeriya

Tinubu ya buƙaci gyara matatun Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci NNPCL ya mayar da hankali kan gyara sauran matatun man Najeriya.

Bola Tinubu ya bukaci NNPCL ya tabbatar da gyara matatun da suke Kaduna da Warri domin kara habaka tattalin arzikin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng