APC da Ganduje Sun Samu Gagarumin Koma Baya, 'Dan Jam'iyya Sun Koma PDP a Bauchi

APC da Ganduje Sun Samu Gagarumin Koma Baya, 'Dan Jam'iyya Sun Koma PDP a Bauchi

  • Wani babban ƙusa a jam'iyyar APC mai adawa a jihar Bauchi, ya tattara kayansa zuwa PDP mai mulki
  • Adamu Bello wanda na kusa da ɗan takarar gwamnan APC a zaɓen 2023 ne, ya ce ya gaji da rashin manufofin ci gaba na jam'iyyar
  • Ya bayyana cewa zai jawo magoya bayansa zuwa jam'iyyar PDP domin ƙara mata ƙarfi a faɗin jihar Bauchi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Jam'iyyar APC ta rasa ɗaya daga cikin manyan jiga-jiganta a jihar Bauchi, wanda ya koma PDP.

Fitaccen jigo a APC a Bauchi, Adamu Bello, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar PDP mai mulki a jihar tun bayan zaben 2019.

Kusa a APC ya koma PDP a Bauchi
Jigon APC ya sauya sheka zuwa PDP a Bauchi Hoto: @OfficialAPCNg, @OfficialPDPNig
Asali: Facebook

Jigon APC ya koma PDP a jihar Bauchi

Jaridar Daily Trust ta ce Adamu Bello, wanda tsohon ɗan majalisar jiha ne kuma tsohon shugaban ƙaramar hukumar Giade, makusanci ne ga Saddique Baba Abubakar, ɗan takarar gwamna a jam’iyyar APC a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa ya ba PDP sirrin kayar da Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adamu Bello ya fito ne daga ƙaramar hukumar Giade ta jihar Bauchi.

Ana dai kallon ficewar tasa a matsayin wani gagarumin koma baya ga jam’iyyar APC a jihar Bauchi, musamman a yankin arewacin jihar, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin APC ta samu nasara a Giade a zaɓen 2023.

Meyasa Adamu Bello ya koma PDP daga APC?

Da yake jawabi yayin ganawarsa da gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya bayyana cewa ya yanke shawarar komawa PDP ne, saboda rashin gamsuwa da yadda APC ba ta da wata manufa ta ci gaban Najeriya.

Adamu Bello ya ce, bayan kasancewa tare da jam’iyyar tun kafuwarta, ya ji takaicin yadda ta kasa samar da wani tsari mai inganci domin ci gaban ƙasar nan.

Ya kuma yaba da irin ayyukan raya ƙasa da aka gudanar a Bauchi, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bala Muhammad.

Adamu Bello ƙara da cewa zai kawo magoya bayansa zuwa PDP, ta yadda za a ƙarawa jam’iyyar ƙarfi a Giade da kuma faɗin jihar.

Kara karanta wannan

"Tinubu ne babbar matsalarmu," Tsohon ɗan takarar gwamna ya soki shugaban ƙasa

Jam'iyyar APC ta gamu da cikas a Rivers

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata babbar kotun jiha da ke birnin Port Harcourt a bayar da umarnin wucin gadi na dakatar da jam'iyyar APC daga gudanar da zaɓuka a Rivers.

Umarnin kotun da aka bayar ranar 19 ga Nuwamba, 2024, ya dakatar da kwamitin gudanarwa na APC daga ci gaba da zaɓukan da ya fara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng