Sojoji Sun Gano Masu Kawo Cikas Wajen Shawo kan Matsalar Tsaro a Najeriya

Sojoji Sun Gano Masu Kawo Cikas Wajen Shawo kan Matsalar Tsaro a Najeriya

  • Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya ya koka kan matsalar masu ba ƴan ta'adda kayan aiki da bayanai a ƙasar nan
  • Janar Christopher Musa ya bayyana cewa masu aikata hakan su ne ke kawo cikas a ƙoƙarin shawo kan matsalar rashin tsaro
  • Ya buƙaci hukumomin tsaro da su yi aiki tare domin kawo ƙarshen masu aikata jakan waɗanda ke rura wutar ta'addanci a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana masu kawo cikas wajen shawo kan matsalar tsaro.

Babban hafsan hafsoshin ya bayyana cewa masu kai wa ƴan ta'adda ababen fashewa da masu ba da bayanai, su ne manyan masu kawo matsala a yaƙin da ake yi da ta'addanci a wasu sassan ƙasar nan.

CDS Musa ya koka kan rashin tsaro
Janar Christopher ya bukaci kawo karshen masu ba 'yan ta'adda bayanai Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Janar Christopher Musa ne ya bayyana hakan ne a cibiyar yaƙi da ta’addanci ta ƙasa da ke Abuja, ranar Talata lokacin da yake jawabi yayin buɗe taron kwanaki biyu kan tsaro da shari’a, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kebbi da jami'an tsaro sun samu nasara kan 'yan ta'adda Lakurawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su waye masu rura wutar ta'addanci?

Ya bayyana masu ba da bayanai da kayan aiki ga ƴan ta’adda a matsayin iskar da ke rura wutar ta’addanci da tayar da ƙayar baya, musamman a shiyyar Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, rahoton Punch ya tabbatar.

Babban hafsan hafsoshin tsaron na Najeriya ya bayyana cewa dole ne a kawo ƙarshensu domin kawo kan matsalar rashin tsaro.

"Dole ne mu dubi yadda za mu magance wannan batun na masu ba da bayanai. Domin waɗannan su ne suka haifar da lamarin. Waɗanda ke tallafawa ƴan ta'adda ta hanyar ba su kayan aiki."
"Ina suke samo kuɗin? Ta yaya suke samun kayayyakin? Mun gano cewa idan muka hana su samun waɗannan kayayyakin, ba za su kai labari ba. Mun yi hakan, inda aka samu kusan mutum 200,000 da suka miƙa wuya."
"Saboda haka ina tunanin idan za mu iya maimaita yin haka a ko'ina, za mu samu sakamako mai kyau. Yana da kyau dukkanin hukumomin tsaro mu haɗa hannu mu yi aiki tare."

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa ya ba PDP sirrin kayar da Tinubu a 2027

- Janar Christopher Musa

Sojoji sun ragargaji ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin sama na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun kai farmaki kan ƴan ta'addan Boko Haram.

Dakarun sojojin sun lalata ma'ajiyar abincin ƴan ta'addan, tare da kashe wasu da dama a wani harin da suka kai ta sama a Jubillaram da ke yankin Tumbuns na tafkin Chadi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng