Matatar Fatakwal: Ƴan Kasuwa Sun Hango Farashin da Fetur Zai Iya Komawa a Najeriya
- Dillalan mai sun nuna farin ciki da fara dakon mai da NNPCL ta yi daga matatar Fatakwal bayan watanni 11 da gyarata
- IPMAN da MEMAN sun bayyana cewa kara wadatar man fetur zai haifar da gasa, wanda a karshe zai rage farashin fetur
- A halin yanzu, motocin NNPCL kawai ke loda fetur daga Fatakwal, inda IPMAN ta ce ba a kai ga gayyatar 'yan kungiyar ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
'Yan kasuwar man fetur sun nuna farin ciki kan ci gaba da aikin matatar man Fatakwal, suna ganin hakan zai karfafa gasa, kara wadatar man, da rage farashi.
An ruwaito cewa kusan manyan motoci 100 sun yi layi don loda man fetur daga matatar a ranar Alhamis, bayan watanni 11 da kammala gyaran ta.
"Farashin man fetur zai iya raguwa" – MEMAN, IPMAN
Clem Isong, Sakataren kungiyar MEMAN, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa suna maraba da gasar farashi da samar da fetur daga wurare daban-daban.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Isong ya ce:
“Muna goyon bayan samar da mai daga wurare daban-daban, hakan zai kawo gasa a kasuwa, saukin samun kaya da kuma rage farashin man."
Kungiyar IPMAN ta bayyana farin cikinta da fara tace fetur daga matatar man Fatakwal, tana fatan hakan zai sai farashin man ya karye.
Mai magana da yawun IPMAN na kasa, Alhaji Olanrewaju Okanlawon, ya ce farashin fetur bai canza ba a yanzu, amma suna sa ran nan gaba kadan zai koma kasa da yadda yake yanzu.
Motocin NNPCL kawai ke daukar mai – IPMAN
Shugaban IPMAN, Abubakar Maigandi, ya bayyana cewa a halin yanzu motocin NNPCL kadai ke loda mai a matatar ta Fatakwal, kuma ba a gayyaci ‘ya’yan kungiyar ba tukuna.
“Mun dogara da matatar Dangote a yanzu, kuma ba mu da bayanai kan farashin Fatakwal, amma za mu sanya ido kan farashin a gidajen man NNPCL,”
- inji Maigandi.
Matatar Fatakwal: Tinubu ya jinjinawa NNPCL
Tun da fari, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya kamfanin NNPC murnar nasarar farfado da matatar man Fatakwal tare da fara lodin man fetur.
Shugaba Tinubu ya bukaci kamfanin NNPCL da ya gaggauta aikin sake farfado da matatar man Fatakwal ta biyu da kuma matatun Warri da Kaduna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng