'Muna Neman Dauki': Abin da Gwamnan Kaduna Ya Fadawa Tinubu kafin Ya Tafi Faransa

'Muna Neman Dauki': Abin da Gwamnan Kaduna Ya Fadawa Tinubu kafin Ya Tafi Faransa

  • Gwamna Uba Sani na Kaduna ya gana da Shugaban Kasa Bola Tinubu a Abuja, inda ya gabatar da rahoton ci gaban jihar
  • Uba Sani ya bayyana nasarorin da aka samu wajen magance matsalolin tsaro, tare da neman daukin Tinubu a wasu fannoni
  • Tinubu ya tabbatar da goyon bayansa ga Kaduna, tare da alkawarin ba da hadin kai wajen inganta tsaro da ci gaban jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya gana da Shugaban Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa (Aso Rock) da ke Abuja.

A yayin taron, Uba Sani ya gabatarwa Tinubu rahoto kan kokarin da ake ci gaba da yi domin magance matsalolin tsaro da cigaban jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya fara rabon tirela 100 na tallafin abinci a jihar Borno

Uba Sani ya fitar da sanarwa yayin da ya gana da Shugaba Bola Tinubu
Gwamnan Kaduna ya gabatar da rahoton ci gaban jihar ga Shugaba Bola Tinubu. Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Gwamnan na Kaduna ya sanar da kaiwa Tinubu ziyarar ne kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X a safiyar Laraba, 27 ga Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Uba Sani ya jinjinawa Tinubu

Uba Sani ya sanar da Tinubu gagarumin ci gaba da aka samu wajen yaki da matsalolin Kaduna tare da bada haske kan shirin da aka tsara don inganta rayuwar al’umma.

Gwamnan ya nuna godiya ga shugaba Tinubu saboda goyon bayan da yake bai wa jihar Kaduna, tare da yabawa gudunmuwar gwamnatin tarayya wajen inganta tsaro.

Uba Sani ya jaddada cewa tallafin shugaba Tinubu ya taka rawar gani wajen cimma muradin gwamnatin jihar na kawo canji mai amfani.

Gwamnan Kaduna na neman daukin Tinubu

Baya ga rahoton da ya gabatar, Gwamna Sani ya nemi karin tallafin gwamnatin tarayya a wasu manyan bangarori da ke bukatar kulawa ta gaggawa.

"Yayin da nake gode masa bisa goyon bayan da yake bai wa jiharmu, na kara neman daukinsa a wasu bangarorin da ke bukatar kulawar gaggawa."

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa manufofin Tinubu suka kawo wahala da tsadar rayuwa a Najeriya

- A cewar Uba Sani.

Shugaba Tinubu ya tabbatarwa Gwamna Sani cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tallafawa Kaduna.

Ya yi alkawarin ci gaba da hada kai da gwamnatin jihar domin tabbatar da nasarar sauya yanayin tsaro da ci gaba a Kaduna.

Tinubu ya shilla zuwa kasar Faransa

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu tare da uwar gidansa Sanata Oluremi Tinubu sun shilla zuwa kasar Faransa domin ziyarar aiki.

Fadar shugaban ƙasa ta ce Tinubu ya amsa gayyatar shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, za su tattauna batutuwa da suka shafi ƙasashen biyu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.