Kano: An Kama Masu Karkatar da Tallafin Shinkafar Tinubu Za a Sayar a Kasuwa

Kano: An Kama Masu Karkatar da Tallafin Shinkafar Tinubu Za a Sayar a Kasuwa

  • Gwamnatin Kano ya kama wani shago makare da shinkafar tallafin Bola Tinubu da ake shirin karkatarwa zuwa kasuwa
  • Shugaba hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da rashawa na jihar, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado ya tabbatar da haka
  • Ya bayyana cewa an kafa buhunan shinkafa sama da 16,000 da ake juyawa buhu zuwa wanda za a shigar wasu daga kasuwannin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Hukumar karbar korafe korafe da yaƙi da cin hanci ta Kano (PCACC) ta kai samame wani dakin ajiya inda ake zazzage shinkafar da gwamnati ta bayar a matsayin tallafi.

Hukumar ta gano yadda ake sakewa shinkafar tallafin buhu, kuma an kama buhuna 16,800 da ake sauyawa buhu domin sayarwa a kasuwanni.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta kammala shirin cefanar da matatun mai 4 mallakin Najeriya

Shinkafa
An kama tallafin shinkafar Tinubu a Kano Hoto: Ibrahim Khalil Adam Bagwai
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ana zargin cewa shinkafar tallafin da gwamnati ta bayar a lokacin azumin Ramadan na shekarar da ta gabata ce aka boye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana sayar da shinkafar Tinubu a Kano

Channels Televsion ta ruwaito cewa buhunan da aka juye shinkafar na dauke da hoton shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

An gano shagon ajiyar shinkafar Tinubu a titin Hotoro Ring, kusa da Farin Masallaci a cikin manyan motocin dakon kaya guda 28.

Gwamnatin Kano ta binciko shinkafar Tinubu

Shugaban hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci ta Kano (PCACC), Barista Muhyi Magaji Rimin Gado ya fadi yadda aka kai ga gano shago makare da shinkafar tallafi.

Barista Muhyi Magaji Rimin Gado ya ce;

“Za mu gudanar da cikakken bincike don gano duk wadanda ke da hannu a ciki. Yanzu haka, mun kama mutum guda, kuma za mu tabbatar mun gano duk waɗanda ke da alaƙa da wannan aikin.

Kara karanta wannan

Duba marasa lafiya kyauta ya tsokano bala'i, an kwantar da daruruwan mutane a asibiti

"Za mu ɗauki duk matakan doka don hana irin wannan daga faruwa nan gaba."

An kama barawon kayan masallaci a Kano

A baya kun ji cewa jami'an hukumar tsaron fararen hula reshen jihar Kano sun damke wani matashi da aka kama da batirin wutar sola da aka sanya a wani masallacin Juma'a.

Jami'an NSCDC na tuhumar matashin mai suna Murtala Aliyu da sata, inda ya amsa cewa ya taba dauke wasu makudan kudi daga masallacin Juma'a a Dakata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.