Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Adadin Fetur da Matatar Fatakwal za Ta Samar a Kullum
- Gwamnatin tarayya ta bayyana irin shirin da aka yi na jigilar man fetur da matatar Fatakwal za ta rika tacewa
- A ranar Talata ne kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya sanar da kammala gyaran matatar, kuma ta fara aikin tace danyen mai
- Mashawarcin Tinubu na musamman kan harkokin yada labarai, Sunday Dare ya ce motoci 200 ne za su rika lodi a kullum
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Gwamnatin tarayya bayyana cewa ana sa ran manyan motocin dakon mai guda 200 za su rika lodin tacaccen fetur a kullum daga matatar mai ta Fatakwal.
Mashawarcin shugaban kasa na musamman kan harkokin sadarwa da hulda da jama’a, Sunday Dare ne ya bayyana haka a ranar Talata.
Hadimin shugaban ya wallafa a shafinsa na X cewa an gyara sashen matatar da ya samu matsala, kuma ta fara aiki kamar yadda ya dace.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a fara jigilar fetur daga matatar Fatakwal
Channels Television ta ruwaito cewa mashawarcin shugaba Tinubu kan harkokin yada labarai, Sunday Dare ya ce matatar Fatakwal da aka gyara za ta fara fitar da fetur.
Ya ce matatar na da karfin tace ganga 60,000 na danyen mai a kowace rana, kuma an shirya yadda za a fara jigilar man daga jihar Ribas.
Za a samu karin fetur daga matatar Fatakwal
Sunday Dare ya bayyana cewa gyara matatar Fatakwal zai farfado da fatan da yan kasar nan ke da shi na samun cigaba.
Ya kara da fadin;
"Ana sa ran manyan motocin dakon albarkatun mai guda 200 za su rika daukar kayayyaki kullum daga matatar, abin da ke sake ba da fata ga Najeriya,"
Matatar Fatakwal ta fara aikin tace fetur
A wani labarin, mun ruwaito cewa bayan shafe tsawon lokaci ana sanya ranar da matatar Fatakwal mallakin kamfanin NNPCL za ta fara aiki, hukumomi sun ce an gama gyara.
Ana sa ran matatar za ta rika fitar da gangar danyen mai 600,000 a kullum, wanda aka fara sa rai da cewa zai kawo saukin farashin litar fetur da wadata jama'ar kasar nan da mai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng