"Tare Muka Kafa APC": Tinubu Ya Ajiye Bambancin Siyasa a Gefe, Ya Jinjinawa Atiku
- Shugaba Bola Tinubu ya taya tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, murnar cikarsa shekaru 78 a duniya
- Tinubu ya yabawa Atiku kan rawar da ya taka wajen cigaban Najeriya, musamman tun dawowar farar hula a 1999
- Duk da sabanin siyasa da ke a tsakaninsu, shugaban ya roki roki Allah ya kara wa Atiku lafiya, nisan kwana da farin ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya jinjinawa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
A ranar 25 ga watan Nuwamba ne Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP a 2023 ya cika shekaru 78 da haihuwa.
Tinubu ya aikawa Atiku sakon ne ta hannun mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Sunday Dare, wadda Olusegun Dada ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya jinjinawa Atiku Abubakar
A cikin sanarwar, Tinubu ya jinjina Atiku Abubakar kan rawar da ya ce ya taka wajen bunkasa dimokuradiyya a Najeriya.
Tinubu ya yaba da irin gudunmawar da Atiku ya bayar tun dawowar mulkin farar hula a 1999, tare da jinjinawa himmarsa wajen cigaban kasa.
Ya kuma tuna lokutan da suka yi aiki tare da Atiku a matsayin wadanda suka kafa jam’iyyar APC, inda suke neman inganta makomar Najeriya.
Shugaba Tinubu ya kuma bayyana Atiku a matsayin mai kishin jama’a da sadaukarwa, yana rokon Allah ya kara masa lafiya da farin ciki.
Rikicin siyasa tsakanin Tinubu, Atiku
Duk da tarihin hadin kansu, Atiku ya sha sukar gwamnatin Tinubu, yana dora alhakin matsalolin da kasar ke fuskanta a kanta.
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa Tinubu bai cika mayar da martani kai tsaye kan sukar Atiku ba, sai dai tawagar yada labaransa na aiwatar da hakan.
An rahoto cewa Atiku da Tinubu sun ci gaba da rikicin siyasa 'yan kwanaki bayan da aka samu sulhu a yayin bikin auren 'yar Sanata Danjuma Goje.
PDP, Tambuwal sun yabawa Atiku
A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar PDP da tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal sun yi ruwan kalaman yabo ga Atiku Abubakar.
Yayin da ya cika shekaru 78 a duniya, PDP da Tambuwal sun ce Atiku ya daidaita tattalin arzikin kasar a lokacin da yake mataimakin shugaban kasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng