Farfado da Matatar Fatakwal: Tsohon Sanata Ya Fadi Fatansa kan Farashin Fetur
- Tsohon Sanata, Shehu Sani ya bayyana jin dadi ganin yadda matatar Fatakwal ta fara tace danyen fetur kamar yadda ya dace
- Tsohon 'dan majalisa ya ce akwai bukatar shugaban kamfanin NNPCL ya waiwayi matatar da ke Kaduna domin a farfado da ita
- Kwamred ya kara da fadin fatansa na samun saukin farashin litar fetur da ya jefa jama'ar kasar nan a cikin mawuyacin hali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya bayyana abin da ya ke fatan farfado da matatar Fatakwal zai haifar.
A yau ne kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya shaida cewa matatar da aka jima ana dakon ta fara aiki, ta fara tace danyen fetur.
A sakon da ya wallafa a shafiinsa na X, Shehu Sani ya ce ana fatan za a farfado da matatar da ke Kaduna, ta fara tace danyen fetur kamar ta Fatakwal.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata ya yi maganar dawowar matatar Fatakwal
Sanata Shehu Sani ya ce ya na fatan yan Najeriya za su samu saukin farashin man fetur bayan matatar Fatakwal ta fara aiki a yau.
Ya ce akwai bukatar cewa fara aikin da matatar ta yi zai saukaka rayuwar 'yan Najeriya, musamman a yanzu da su ke a cikin mawuyacin hali.
Fatan Sanata Shehu Sani kan matatar Kaduna
Sanata Shehu Sani ya bayyana fatan cewa kamfanin NNPCL zai waiwayi matatar Kaduna domin ta fara aikin tace danyen fetur.
Haka kuma ya yaba da kokarin shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari na farfado da matatar Fatakwal, musamman ganin cewa Najeriya ba ta iya tace albarakatun da ta ke samarwa.
Tsohon Sanata ya yabawa gwamnati kan tsaro
A wani labarin, kun ji cewa tsohon Sanata Shehu Sani ya bayyana gamsuwa kan yadda ofishin mashawarcin shugaban kasa ke kokari wajen magance rashin tsaro da ya addabi Arewa.
Haka kuma tsohon Sanatan ya yaba da jajircewar Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa ya yi kokari matuka idan aka kwatanta da magabatansa da su ka rike ofishin da ya ke a yanzu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng