Bayan Mutuwar Sanata, Kawu Sumaila Ya Karbi Mukaminsa, An Yi Zargin Siyasa a Nadin

Bayan Mutuwar Sanata, Kawu Sumaila Ya Karbi Mukaminsa, An Yi Zargin Siyasa a Nadin

  • Sanata Kawu Sumaila daga jihar Kano ya samu mukamin shugaban kwamitin albarkatun mai a Majalisar Dattawa
  • Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio shi ya nada Sumaila domin maye gurbin marigayi Sanata Ifeanyi Ubah da ya rasu
  • Wannan nadin ya jawo maganganu duba da Sumaila dan NNPP ne kuma wasu na ganin dan Kudu ya kamata a nada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Dan Majalisar Dattawa, Sanata Kawu Sumaila ya samu mukamin shugaban kwamitin abarkatun mai.

Kawu Sumaila ya maye gurbin marigayi Sanata Ifeanyi Ubah wanda ya rasu a Landan a watan Yulin 2024 kuma aka birne shi a makon jiya.

An nada Kawu Sumaila babban mukami a Majalisar Dattawa
Sanata Kawu Sumaila ya samu mukamin shugaban kwamitin albarkatun mai. Hoto: Sen. Kawu Sumaila.
Asali: Facebook

Sanata Sumaila ya samu babban mukami a Majalisa

Tribune ta ce nadin Sumaila ya jawo ce-ce-ku-ce inda wasu ke ganin bai dace ya samu mukamin ba.

Kara karanta wannan

Majalisa ta fara tuhumar Tinubu saboda batun karbo aron Naira Tiriliyan 1.7

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu na ganin cewa ya kamata dan Kudancin Najeriya ne zai maye gurbin marigayi Ubah duba da Sumaila dan jihar Kano ne.

Sanata Sumaila da ke wakiltar Kano ta Kudu ya samu mukamin ne bayan shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ya nada shi.

Sai dai shugaban kwamitin aikace-aikace a Majalisar, Sanata Sunday Karimi ya ce nadin Sumaila alheri ne.

Karimi ya ce nadin zai zama ribar kafa ga jam’iyyar APC da kuma shugaba Bola Tinubu a zabe mai zuwa.

Ana zargin akwai siyasa a nadin Sumaila

“Ba kowane lokaci ba ne za mu soki matakai da ake dauka, wasu matakai musamman irin wadannan suna da muhimmanci.”
“Kano jiha ce ta yan adawa amma APC na son kwace ta, yadda aka yi wannan nadin na sanata mai kwarewa hakan wani yunkuri ne na mamaye jihar da neman magoya baya.”
“Wannan mataki zai zama alheri ga jam’iyyar APC da kuma siyasar Shugaba Bola Tinubu a zabukan da ke tafe.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban ƙasa ta yi martani ga kalaman malamin addini kan sukar Tinubu

- Sunday Karimi

Kawu Sumaila ya ja kunnen Abba Kabir

Kun ji cewa yayin da rigimar jam'iyyar NNPP ke kara ƙamari, Sanata Kawu Sumaila ya yi magana inda ya shawarci Abba Kabir.

Sanata Sumaila da ke wakiltar yankin Kano ta Kudu ya ce ya kamata Abba ya sani ba iya yan Kwankwasiyya ba ne kaɗai a jihar.

Sumaila ya ce babban cin amana shi ne bijirewa Allah da ya yi masa gata a rayuwarsa inda ya ba shi shawara kan mulki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.