Zargin Bata Suna: Hamdiyya Ta Fadi Abin da Faru da Ita a Sokoto bayan Fitar da Bidiyo
- Matashiya yar TikTok a jihar Sokoto ta bayyana abubuwan da suka faru da ita bayan fitar da wani bidiyo kan ayyukan ta'addanci
- Matashiyar mai suna Hamdiyya Sidi Shareef ta fayyace komai kan dalilin yin bidiyon da kuma cin zarafinta da jami'an tsaro suka yi
- Hakan ya biyo bayan sakin bidiyo kan ayyukan ta'addanci wanda gwamnatin jihar ta cafke ta da zargin bata sunan Gwamna Ahmed Aliyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Sokoto - Al'ummar Najeriya suna cigaba da tofa albarkacin bakinsu kan cafke yar TikTok, Hamdiyya Sidi Shareef da aka yi.
Hakan ya biyo bayan wallafa wani faifan bidiyo da ta yi kan hare-haren yan bindiga da kuma cin zarafin mata da yara da ke yi.
Hamdiyya ta bayyana kuncin da ta shiga
A cikin wani faifan bidiyo da shafin Brekete Family ya wallafa a Facebook, Hamdiyya ta yi bayanin yadda lamarin ya kasance.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hamdiyya ta faro yadda ta samu mai garin Sabon Birni,inda ta bukaci yin bidiyo kan abubuwan da ke faruwa har ya amince mata.
A cikin bayaninta, Hamdiyya ta ce bayan wallafa bidiyon yan banga sun zagaye gidansu da motoci da babura inda suka yi ta dukan yan uwanta har sai da suka bar numfashi.
Daga bisani an dauke ta a mota domin zuwa ofisoshinsu suka yi ta dukanta a mota da cewa ta bata sunan Gwamna Ahmed Aliyu.
Barazana da yan sanda, sa-kai suka yi mata
"Sun yi ta zagina inda wani ya ce manin jaka, dabba ko ubana bai kai ya ɓaci gwamna ba bare ni, na ce ni ba bacinsa na yi ba idan har shi zai ji haushi su wadanda abin ke faruwa a kansu fa."
"Ya ce lokacin da Hon. ya sa a nemo ni da ya hadu da ni harbe ni zai yi a haka rami a birne ni a ce yan bindiga ne suka yi ajalina."
- Hamdiyya Sidi
Yar gwagwarmayar ta kara da cewa yan banga sun kai ta bayan kanta, suka tube mata hijabi da barazanar yi mata fyade idan ya so ta je ta ba da labari.
Ta ce jagoran yan bangan ya ce mata sai ta je gidan yari ko kuma duk inda suka hadu shi ne ajalinta saboda a kan Gwamna bai san rayukan da ya dauka ba.
Daga bisani, Hamdiyya ta ce an wuce da ita ofishin yan sanda a Wurno, aka ci zarafinta sannan wani dan sanda ya yi mata barazanar kisa idan ta fadi abin da suka yi mata.
Hamdiyya ta kara cewa daga bisani an kai ta kotu har aka ba da belinta amma ta koma gidan kakarta kafin kurar da ta taso ta lafa da kuma tseratar da rayuwarta.
Ta ce wata rana ta fita karbo wayarta ba ta san ya aka yi ba ta fara jin duka ta ko ina inda wasu ke cewa a yi mata fyade wasu kuma suka ce kashe ta aka ce a yi ba fyade ba.
Hamdiyya: Amnesty ta caccaki gwamnatin Sokoto
Kun ji cewa Kungiyar Amnesty International ta zargi gwamnatin Sokoto da kokarin dakile gwagwarmaya a fadin jihar.
Wannan na zuwa bayan wasu mutane sun dauki yar gwagwarmaya, Hamdiyya Sidi tare da yi mata dukan kawo wuka.
Hamdiyya Sidi ta saki bidiyo ta na tuhumar yadda gwamna Ahmed Aliyu ya bar yan ta'adda na cin zarafinsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng