Duba Marasa Lafiya Kyauta Ya Tsokano Bala'i, An Kwantar da Daruruwan Mutane a Asibiti
- Gwamnatin Abia ta fara daukar mataki wajen ceto wasu daga cikin mazauna jihar bayan kwantar da su a gadajen asibitoci
- Mutane da dama ne su ka shiga matsala bayan sun karbi magunguna kyauta da wata kungiya ta shirya gudanarwa a jihar
- Kwamishinan lafiya ya shawarci jama'a da su guji zuwa wuraren karbar magunguna kyauta ba tare da sahalewar gwamnati ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Abia - An kwantar da mutane da dama a asibitoci daban-daban biyo bayan wani aikin duba lafiyarsu kyauta a garin Abiriba da ke karamar hukumar Ohafia ta jihar Abia.
Kwamishinan lafiya na jihar, Ogbonnaya Uche, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa ranar Litinin a Umuahia.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Kwamishinan ya danganta kwantar da jama’a asibitocin bayan magungunan da aka ba su karbe su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jama’a sun shiga uku a jihar Abia
Daily Post ta wallafa cewa jama’a sun gamu da cikas bayan lafiyarsu ta tabu garin karbar magani kyauta daga wadansu kungiyoyi.
Ma’aikatar lafiya ta jihar ta tabbatar wa jama’a cewa ma’aikatan kiwon lafiya suna aiki tukuru don ceto wadanda su ka fada a cikin iftila’in.
Gwamnatin Abia ta fara binciken magungunan
Gwamnatin jihar ta jaddada kudirinta na kula da lafiyar mazauna yankin tare da karfafa guiwar masu sha'awar hada kai a fannin kiwon lafiya da su nemi amincewar ma'aikatar.
A cewar kwamishinan lafiya na jihar, Ogbonnaya Uche, ya bayyana cewa;
“Ma’aikatarmu ta damu matuka da illar da aka samu bayan bayar da magani kyauta a jihar. Ya kamata jama'a su yi taka-tsan-tsan game da masu shirya abubuwan kiwon lafiya da ba a amince da su ba."
Gwamnan Abia ya yi garanbawul
A baya mun ruwaito cewa gwamna Alex Otti na Abia ya kori shugaban jami'ar jihar da ke Uturu (ABSU), Farfesa Onyemachi Ogbulu daga aiki tare da maye gurbinsa da Farfesa Ndukwe Okeudo.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Okey Kanu ya ce gwamnan ya amince da hakan ne a taron majalisar zartarwar, inda aka kara wasu sababbin nade-naden a kokarin yin garanbawul.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng