Ana Zargin Lakurawa Sun Yadu Zuwa Kaduna, Tinubu Ya Nemo Hanyar Dakile Matsalar

Ana Zargin Lakurawa Sun Yadu Zuwa Kaduna, Tinubu Ya Nemo Hanyar Dakile Matsalar

  • Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin kara tura jami'an tsaro yankunan da yan kungiyar Lakurawa suka addaba
  • Ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ya tabbatar da haka, ya ce sojojin sama sun yi ruwan wuta kan yan ta'addan
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin yan kungiyar sun fara yaɗuwa zuwa jihohin Niger da kuma Kaduna a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Yayin da ake fargabar yaɗuwar yan kungiyar Lakurawa, Gwamnatin Tarayya za ta kara tura dakarun sojoji.

Gwamnatin Tarayya za ta tura wasu dakarun yayin da ake zargin sun watsu zuwa jihar Niger har ma da Kaduna.

Za a tura karin sojoji da Lakurawa suka yadu a Arewa
Gwamnatin Najeriya za ta sake tura sojoji da ake zargin Lakurawa sun yadu zuwa Kaduna da Niger. Hoto: Muhammad Badaru Abubakar, Dr. Bello Matawalle.
Asali: Facebook

Ministan tsaro zai kawo karshen yan Lakurawa

Punch ta ruwaito cewa yan kungiyar Lakurawa sun fi karfi a yankin Arewa maso Yamma musamman jihohin Sokoto da Kebbi.

Kara karanta wannan

Abia: Dakarun sojoji sun far wa ƴan Bindiga, an fara musayar wuta mai zafi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ya ba yan jihohin Sokoto da Kebbi tabbacin murkushe yan Lakurawa.

Badaru ya ba da tabbacin ne a Sokoto yayin da aka ruwaito cewa sun fara yaɗuwa zuwa Niger da Kaduna, cewar Tribune.

Yadda sojoji suka fatattaki yan kungiyar Lakurawa

Badaru ya ce dakarun sojoji sun ba Lakurawa wahala yayin da aka tura daruruwan jami'an tsaro a yankin.

"Kun ji shugaban karamar hukumar da Lakurawa suka kai hari yana cewa an jibge jami'an tsaro a yankunansu."
"An fatattaki yan kungiyar Lakurawa a yankin saboda jajircewa na jami'an sojojinmu da ke aiki ba dare ba rana."
"Ku na sane da irin nasarar da sojojin sama suka samu kan Lakurawa inda suka sake musu bama-bamai da yanzu suka rasa matsuguni."

- Muhammad Badaru Abubakar

Nijar: Lakurawa sun hallaka mutane da dama

Kun ji cewa wani sabani ya jawo matsala yayin da wasu mayakan kungiyar Lakurawa su ka kashe mazauna jamhuriyyar Nijar.

Kara karanta wannan

'Karshen Turji da yan bindiga ya kusa': Ministan tsaro bayan karbar jirage daga Turkiyya

Mutane akalla biyar ne su ka riga mu gidan gaskiya bayan Lakurawa sun dirar masu saboda an hana su aure.

Lamarin ya afku a garin Gueza da ke Dosso a jamhuriyyar Nijar inda daya daga cikin shugabannin Lakurawa ya je neman aure.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.