Sabon Mafi Karancin Albashi: Gwamna Uzodimma Zai Fara Biyan Ma'aikata N70,0000

Sabon Mafi Karancin Albashi: Gwamna Uzodimma Zai Fara Biyan Ma'aikata N70,0000

  • Gwamnan Imo, Hope Uzodimma ya amince da fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi na N70,000 ga ma'aikatan jihar
  • Shugabannin ƙungiyoyin kwadago sun tattauna da gwamnan kafin a yanke shawarar inganta walwalar ma'aikatan jihar Imo
  • Gwamnan ya amince da biyan albashi biyu a Disambar kowace shekara tare da sanya masu ritaya a shirin lafiya na SHSS

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Imo - Gwamna Hope Uzodimma ya sake tabbatar da alkawarin gwamnatin jihar Imo na kula da walwalar ma'aikata da wadanda suka yi ritaya.

Gwamnatin Hope Uzodimma ta amince da aiwatar da sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000 ga ma'aikatan jihar Imo.

Gwamnan Imo ya yi magana yayin da ya amince da sabon albashin N70,000
Gwamnan Imo zai fara biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000. Hoto: @Hope_Uzodimma1, @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

Gwamnan jihar ne ya sanar da wannan ci gaban a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a safiyar ranar Talata, 26 ga Nuwambar 2024.

Kara karanta wannan

NLC ta ba Gwamna Radda wa'adi kan shiga yajin aiki a Katsina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Imo ya amince da albashin N70000

Wannan shawarar ta biyo bayan tattaunawa mai zurfi da shugabannin ƙungiyoyin kwadago, wanda ke nuna ƙudurin gwamnati na inganta rayuwar ma'aikata.

Gwamna Uzodimma ya ce an amince da karin kashi 10% ga waɗanda ke kan tsarin albashi na haɗaɗɗen albashi, don tabbatar da daidaito a dukkanin matakan albashin jihar.

Baya ga aiwatar da sabon mafi karancin albashin, gwamnatin Imo ta tabbatar da cewa ma'aikatan da suka samu karin girma za su fara ganin sabon albashinsu.

Gwamnan Uzodinma zai biya albashi 2 a Disamba

Sanarwar Gwamna Uzodimma ta ce za a ci gaba da biyan albashin watanni 13 a kowace shekara (albashi biyu a Disamba), wanda zai ƙara inganta walwalar ma'aikata.

Gwamnatin Uzodimma ta kuma amince a sanya tsofaffin ma'aikatan jihar cikin shirin kiwon lafiya na jihar, don tabbatar da sun samu kula da lafiya kyauta.

Kara karanta wannan

Gwamna ya umarci cafke wasu ma'aikatan lafiya a jiharsa

Hakazalika, gwamnan jihar ya ce zai fara biyan kudin ritaya ga rukuni na gaba na masu ritaya, wanda ke nuna ƙudurin gwamnati na mutunta wadanda suka kammala aiki.

Gwamnan Anambra ya amince da albashin N70000

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya amince da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata a jihar.

Gwamna Soludo ya bayyana cewa gwamnatinsa na kokarin ganin cewa ma'aikata ba su samu albashin da ya gaza N70,000 ba, inda ya ce zai iya biyan tsakanin N78,000 zuwa N84,000.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.