Kabiru Gombe Ya Soki Muslim Muslim da Aka Tallata, Ya Kira Tinubu 'Dan Ci da Addini
- Sheikh Muhammad Kabiru Gombe ya yi magana kan zargin da ake yi wa malamai cewa suna ci da addini a Najeriya
- Malamin ya yi bankada, ya ce ainihin masu ci da addini ba su wuce Bola Tinubu da Kashim Shettima da mukarrabansu ba
- Wannan na zuwa ne yayin da ake ganin Sheikh Sani Yahaya Jingie na kokarin kare muradun gwamnatin Bola Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Gombe - Yan Najeriya da dama na sukar wasu malaman Musulunci da cewa suna ci da addini musamman a wannan gwamnati.
Sai dai Sheikh Kabiru Gombe ya yi zazzafar martani inda ya fayyace asalin wadanda suke ci da addini a Najeriya.
Sheikh Kabiru Gombe ya fusata da zargin ci da addini
Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da Abubakar Umar ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Kabiru Gombe ya koka kan yadda yan Najeriya ke zargin malamai da ci da addini duk da ba su ci komai ba a gwamnatin.
Shehin malamin ya ce babu wadanda suka fi ci da addini kamar Bola Tinubu da Shettima da sauran ministoci a gwamnatin.
Kabiru Gombe ya bayyana masu ci da addini
"Shugaban 'yan ci da addini a Najeriya shi ne Shugaba Bola Tinubu, ku fada mani da me ya ci zabe? domin me kuka zabe shi?"
"Mene aka ce muku lokacin zabe? Muslim Muslim, da me ya ci kenan? To mu da me muka ci?"
"Na biyu shi ne mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, su ne manyan-manyan masu ci da addini ku zo kuna ce mana malamai suna ci da addini."
- Sheikh Kabiru Gombe
Sheikh Kabiru Gombe ya ce duk minista da aka naɗa a wannan gwamnati da addini yake ci saboda da addini aka kafa gwamnatin.
Malamin ya ce duk masu rike da ofisoshi a gwamnati da gwamnonin Arewa su ne manyan masu ci da addini.
Liyafa: Sheikh Kabiru Gombe ya wanke malamai
Kun ji cewa Sheikh Kabiru Gombe ya wanke malaman addinin musulunci kan halartar diyar Rabiu Kwankwaso da dan Dahiru Mangal.
Wannan ya biyo bayan martanin da su ka sha bayan an hango malaman a bikin 'dinner' Aisha Kwankwaso da Fahad Mangal.
Sheikh Kabiru Gombe ya jaddada cewa alakar addini ce ta sa malaman su ka halarci liyafar ba wasu dalilai na daban ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng