N48trn: An Sanya Ranar da Tinubu Zai Gabatar da Kasafin 2025 ga Majalisar Tarayya
- Ana sa ran shugaban kasa Bola Tinubu zai gabatar da kasafin kudin 2025 gaban majalisar tarayya a ranar Laraba, 27 ga Nuwamba
- Sakataren sashen bincike da bayanai na majalisa, Dakta Ali Barde Omoru ya sanar da shirin Tinubu na gabatar da kasafin kudin
- Shugaba Tinubu zai gabatar da Naira tiriliyan 48 gaban majalisar tarayyar, inda albashin ma'aikatan tarayya zai lakume N6.5trn
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Majalisar tarayya ta bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya kammala shirye-shiryen gabatar da kasafin kudin 2025.
Sakataren sashen bincike da bayanai na majalisar tarayyar, Dakta Ali Barde Omoru ya sanar da lokacin da Tinubu zai gabatar da kasafin.
Tinubu zai gabatar da kasafin 2025
Jaridar Daily Trust ta rahto Dakta Ali ya ce Tinubu zai gabatar da kasafin Naira tiriliyan 47.9 gaban majalisar a ranar Laraba, 27 ga Nuwambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dakta Ali ya sanar da cewa shugaban kasar zai gabatar da kasafin ne a zauren majalisar da ya kunshi bangarorin majalisar tarayyar biyu - sanatoci da 'yan majalisar wakilai.
Sakataren ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tabbatarwa 'yan jaridar shirin gabatar da kasafin, tare da neman sunayen wadanda za a bari su shiga zauren taron.
Majalisar tarayya ta yi magana tun tuni
Tun kafin sanarwar Dakta Ali, majalisar dattawa ta bayyana cewa mai yiwuwa Shugaba Bola Tinubu zai gabatar da kasafin kudin 2025 a wannan mako, inji rahoton Punch.
A cewar mai magana da yawun majalisar dattawa, Yemi Adaramodu (APC, Ekiti ta Kudu), kwamitin kudi zai gana da ma’aikatu, bangarori da hukumomi.
Ya ce, “Watakila shugaban kasa zai gabatar da kasafin kudin 2025 a wannan makon. Tuni dama kwamitin kudi ya fara aiki kan daftarin MTEF."
Tinubu ya gabatarwa majalisa daftarin MTEF
Tun da fari, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da daftarin tsare tsaren kasafin kudin 2025 zuwa 2027 na gwamnatin tarayya (MTEF/FSP) ga majalisar wakilai.
Bayanan da ke cikin daftarin ne suka sanya aka amince da N47.9trn a matsayin kasafin 2025, inda albashin ma'aikatan tarayya zai lakume N6.5trn a cikin kasafin.
Asali: Legit.ng