"Babu Amincewar Majalisa": Sanata Ya Tona Yadda Aka Sayawa Tinubu Sabon Jirgin Sama
- Sanata Enyinnaya Abaribe ya yi ikirarin cewa shugaba Bola Tinubu ya sayi sabon jirgin sama ba tare da izinin majalisar tarayya ba
- Dan majalisar dattawan daga Abia ta Kudu ya ce babu wata takarda ta neman izinin sayen jirgin da aka gabatarwa majalisar
- Sanata Abaribe ya ce har aka kammala cinikin jirgin aka kawosa Najeriya, majalisar tarayya ba ta sa hannu cikin harkallar ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Sanata Enyinnaya Abaribe, mai wakiltar Abia ta Kudu, ya zargi Bola Tinubu da kaucewa neman izinin majalisa wajen sayen jirgin shugaban kasa.
A watan Agusta ne fadar shugaban kasa ta kaddamar da wani sabon jirgin sama kirar Airbus A330 da aka saya wa Shugaban kasa Bola Tinubu.
Da yake magana a Channels TV a ranar Litinin, Sanata Abaribe ya tabbatar da cewa ba a kai bukatar sayen jirgin gaban majalisar tarayya ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Bai nemi izini ba' - Sanata ya soki Tinubu
Dan majalisar dattawan ya ce:
"Ni dan majalisa ne, kuma zan tabbatar muku cewa babu wanda ya kawo wata bukata ta neman izinin sayen wannan jirgin."
Sanatan ya bayyana cewa bai san komai game da batun ba, yana mai cewa, "a duk zamana majalisar, ban taba ganin wata takarda a kai ba."
Abaribe ya nuna damuwa cewa rashin neman izinin majalisar yana rage tasirin aikin duba ayyukan bangaren zartarwa da ya kamata su yi.
Sanata Abaribe ya kare alakar majalisa da FEC
Ya kuma koka kan yadda jama’a ke kallon majalisar dokoki a matsayin wadda ke yin biyayya kawai, saboda rashin nasarorin da ake gani a kasa.
A cewarsa, ‘yan majalisa na ganin kokarinsu na kalubalantar zartarwa ba ya haifar da da mai ido don haka ne suke neman sulhu da bangaren zartarwar.
Maganganun Sanatan sun jaddada rashin jituwa tsakanin bangarorin zartarwa da na majalisar Najeriya, musamman a kan gaskiya da cin gashin kai.
Jam'iyyu sun soki Tinubu kan sayen jirgi
A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyun adawa a Najeriya sun caccaki shugaba Bola Tinubu kan sayen sabon jirgin sama yayin da tattalin kasar ke tangal tangal.
Jagororin jam'iyyun adawa irinsu PDP, LP sun ce bai kamata Tinubu ya sayi sabon jirgi ba yayin da 'yan kasar ke fama da tsadar rayuwa da hauhawar farashin kaya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng