Gwamna Zulum Ya Fara Rabon Tirela 100 na Tallafin Abinci a Jihar Borno

Gwamna Zulum Ya Fara Rabon Tirela 100 na Tallafin Abinci a Jihar Borno

  • Gwamnatin jihar Borno ta kaddamar da rabon tallafin abincin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sahale a kai masu
  • An kai tirelolin masara, gero da dawa ga mutanen Ngala da mamakon ruwa ya raba da sauran sassan jihar na watanni
  • Gwamna Zulum ya yaba da yadda gwamnatin tarayya ta ji kan jama'arta, tare da bayyana karin tallafi ga 'yan Maiduguri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum na Borno ya fara mika tallafin tirelolin abinci da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya aiko ga mutanen jihar.

Ana rabon kayan abincin ne ga mazauna karamar hukumar Ngala biyo bayan mawuyacin halin da jama’a su ka shiga.

Borno
An fara rabon tallafin abincin Tinubu a Borno Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

Gwamna Babagana Umara Zulum ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa daga cikin kayan abincin da Tinubu ya aika akwai masara, gero da dawa.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban ƙasa ta yi martani ga kalaman malamin addini kan sukar Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zulum ya fara rabon abincin Tinubu a Borno

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito gwamna Babagana Zulum ya bayyana cewa tallafin abincin da Tinubu ya aika jihar wani mataki ne na jin kan jama’a.

Yayin da ya ke kaddamar da raba kayan abincin, gwamna Zulum ya ce;

“Wannan gari ya gaza shiga sauran sassan kasar nan har na tsawon watanni hudu saboda mamakon ruwan sama da ambaliya. Babu damar shigo da abinci Ngala. Wannan ya sa mu ka zo a yau domin tallafawa mutanen yankin.”

Zulum ya godewa gwamnatin Bola Tinubu

Gwamnan Borno, a madadin al’umarsa ya mika godiya ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran masu ruwa da tsaki da ke tallafawa mutanen jihar.

Dadin dadawa, gwamnatin tarayya ta bayar da motoci 100 na shinkafa domin tallafawa wadanda ambaliyar Maiduguri ta shafa.”

Tinubu ya mika tallafin abinci

A baya mun ruwaito cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya fara tausayawa halin da yan kasa su ka shiga, ya amince da bayar da tallafin tirelolin shinkafa ga jihohin kasar nan 36.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa manufofin Tinubu suka kawo wahala da tsadar rayuwa a Najeriya

Ministan yada labarai, Bala Muhammad ne ya bayar da tabbacin bayar da tallafin, ya ce manufarsa ita ce rage radadin rayuwa ga masu karafin karfin da ke jin garin a wannan lokaci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.