Yan Sanda Sun Ragargaji Yan Bindiga Suna Tsaka da Harbin Matafiya
- Rundunar yan sanda ta ceto wasu mutane da aka yi nufin garkuwa da su bayan yan bindiga sun bude musu wuta suna cikin tafiya a motoci
- Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a kauyen Dan'aru a kan hanyar Magama zuwa Jibia a karamar hukumar Jibia
- Yan sandan sun yi musayar wuta da yan bindigar kuma sun ceto mutane 14 yayin da biyu suka samu mummunan raunuka saboda harbi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - Wasu yan bindiga da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun bude wuta kan matafiya a karamar hukumar Jibia.
Lamarin ya jawo rundunar yan sanda ta kai wa matafiyan agajin gaggawa inda ta ceto mutane da dama.
Jaridar Leadership ta wallafa cewa kakakin yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ne ya tabbatar da lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan sanda sun kubutar da mutane a Katsina
Wasu yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun bude wuta kan motocin matafiya guda biyu.
Rahoton Channels Television ya nuna cewa rundunar yan sanda ta nufi wajen da gaggawa domin ceto rayuwar matafiyan.
Kakakin yan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Lahadi.
"Shugaban yan sanda a yankin ya jagoranci jami'ai domin yin musayar wuta da yan bindigar.
Hakan ya jawo hana miyagun garkuwa da matafiyan kuma an ceto rayuwar mutane 14.
Matafiya biyu sun samu mummunan harbin bindiga kuma daya ya rasu yana tsaka da karɓar magani a asibiti."
- Kakakin yan sandan Katsina
ASP Aliyu ya tabbatar da cewa a yanzu haka jami'ai sun bazama neman masu garkuwa da mutane bayan sun gudu.
Kwamishinan yan sandan jihar Katsina ya yabawa yan sandan bisa kokarin da suka yi tare da kiran garesu da su cigaba da jajircewa.
An fatattaki Lakurawa a Kebbi
A wani rahoton, kun ji cewa yan ta'addan Lakurawa sun gamu da cikas a yunƙurin da suka yi na satar kayan mutane a jihar Kebbi.
Gwamnatin jihar tare da haɗin gwiwar jami'an tsaro sun samu nasarar daƙile yunƙurin ƴan ta'addar su na satar shanu a wasu ƙauyuka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng