'Ku Ja Jari': Abokin Hamayyar Tinubu a Zaben 2023 Ya ba Matasa 25 Kyautar N7.5m
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi ya ba da tallafin N7.5m ga matasa 25 a Onitsha, domin tallafawa kasuwancinsu
- A taron da Faithspiration Initiative ta shirya, Peter Obi ya jaddada muhimmancin aiki tukuru da jajircewa ga matasan Anambra
- Obi ya yi alkawarin ba mutane biyu karin tallafi a kowane wata daga Janairun 2025, yayin da ya tuno da gwagwarmayar rayuwarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra - Peter Obi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin jam'iyyar LP a 2023 ya gwangwaje matasa 25, kowa ya samu kyautar N300,000.
An ce Peter Obi ya rabawa matasan tallafin kudin da ya kai Naira miliyan 7.5 a garin Onitsha da ke jihar Anambra, a matsayin tallafin sana'a.
Peter Obi ya ba matasa 25 tallafin kudi
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, dan takarar ya ce bayar da tallafin ne a yayin wani taron tattaunawa da Faithspiration Initiative ta shirya a ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Obi ya bayyana cewa tallafin kudin zai taimaka wa matasan wajen bunkasa sana'o'insu daban-daban wanda hakan zai sa su samu riba mai yawa.
Ya tunatar da matasan cewa himma ba ta ga rago, kuma dole sai an tashi tsaye an yi aiki tukuru tare da jajircewa ne za a iya samun nasarar da ake nema
Peter Obi ya ba matasa shawarwari
Ya tunatar da matasan cewa himma ba ta ga rago, kuma dole sai an tashi tsaye an yi aiki tukuru tare da jajircewa ne za a iya samun nasarar da ake nema.
Dan siyasar ya ba matsan labarin gwagwarmayar rayuwasa, inda ya bayyana cewa duk da an haife shi kuma ya girma a Onitsha, nasara ba ta zo masa a cikin sauƙi ba.
Obi ya yi wa wadanda suka shirya taron godiya sannan ya sanar da cewa za a rika ba matasa biyu karin tallafi a kowanne wata daga Janairun 2025.
Peter Obi ya fadi manyan matsalolin Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa dan takarar shugaban kasa a 2023, Peter Obi ya yi ikirarin cewa kotuna da alkalai ne manyan barazana ga dimokuraɗiyyar Najeriya.
Peter Obi ya ce lallai akwai bukatar a kawo gyara a kan yadda alkalai ke gudanar da ayyukansu a Najeriya la'akari da cewa kotuna ne 'yan kasar ke tunanin za su share hawayensu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng