An Zargi Buhari da Tsige Alkalin Alkalai soboda Yin Maguɗin Zaɓe a 2019
- Tsige alkalin alkalan Najeriya, Walter Onnoghen da shugaba Muhammadu Buhari ya yi, ya na cigaba da jawo ce-ce-ku-ce
- Jagoran yan kabilar Ijaw, Edwin Clark ya zargi Muhammadu Buhari da ministan shari'a a lokacinsa da kitsa tsige Onnoghen
- Edwin Clark ya yi zargin cewa Buhari ya tsige alkalin ne domin ya hango alamun zai kawo masa matsala a zaben shekarar 2019
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari na shan suka kan sauya tsohon alkalin alkalan Najeriya, Walter Onnoghen.
Jagoran kabilar Ijaw, Edwin Clark ya ce Buhari ya sauke Onnoghen ne domin ya yi maguɗin zaɓe a 2019.
Business Day ta wallafa cewa Edwin Clark ya fadi haka ne a cikin wata wasika da ya aikawa gwamnatin Bola Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An zargi Buhari kan sauke alkalin alkalai
Jagoran yan kabilar Ijaw, Edwin Clark ya zargi Buhari da shirya makirci wajen sauke tsohon alkalin alkalan Najeriya, Walter Onnoghen.
Edwin Clark ya yi zargin cewa Buhari da ministan shari'a, Abubakar Malami ne suka kitsa sauke Onnoghen.
Clark ya ce abin kunya ne yadda shugaba Buhari ya yi rantsuwa zai tsayar da gaskiya amma ya tsige Walter Onnoghen bisa zalunci.
"Buhari ya kyale shi (Walter Onnoghen) ya zamo alkalin alkalan Najeriya amma daga baya ya hango barazana.
Buhari ya tabbatar da cewa Walter Onnoghen ba zai bari ya yi makirci a zaben 2019 ba, sai ya sauya shi.
Wannan wani abu ne da aka kulla a sirrance tsakanin Buhari da tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami."
- Edwin Clark
Clark ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu a kan ya kaucewa ware wasu shafaffu da mai a mulkinsa.
Vanguard ta wallafa cewa Edwin Clark ya yi addu'ar Allah ya cigaba da kare Walter Onnoghen a duk inda yake.
Gidan soja: Labarin Kanal Fadile da Buhari
A wani rahoton, kun ji cewa lauyan sojoji Kanal Babatunde Fadile ya fadi yadda tsohon shugaba Muhammadu Buhari ya so raba shi da aikinsa.
Kanal Fadile ca ce sun fara haduwa a garin Ibadan, a lokacin Muhammadu Buhari ya na matsayin mai kula da sojojin kasa da ke Oyo.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng