Onnoghen: Buhari ya fattakeni ne bayan an ce masa na gana da Atiku a Dubai

Onnoghen: Buhari ya fattakeni ne bayan an ce masa na gana da Atiku a Dubai

- Tsohon alkalin alkalai, Walter Onnoghen yace Buhari ya kore shi daga aiki ne bayan ya ji rade-radin ya gana da Atiku a Dubai

- Ya kara da cewa, an zargesa da sakin manyan 'yan ta'adda amma kuma tun 1978 ya bar babban kotu

- A 2019 ne shugaban kasa Buhari ya dakatar da Onnoghen bayan an zargesa da kin bayyana dukiyarsa da asusun banki na ketare

Tsohon alkalin alkalai, Mai shari'a Walter Onnoghen, ya bayyana dalilin da yasa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sallameshi.

Onnoghen, wanda aka zarga da kin bayyana kadarorinsa tare da mallakar asusun banki a ketare, an sallameshi daga aiki ana sauran makonni kadan kafin zaben shugaban kasa a 2019.

Daily Trust ta ruwaito cewa, daga bisani kotu ta musamman ta CCT ta yanke masa hukuncin haramta rike ofishin gwamnati na tsawon shekaru 10.

Sallamar Onnoghen ta janyo maganganu daban-daban inda wasu jama'a ke kallon hakan da siyasa zalla.

KU KARANTA: Boko Haram Sun Tsinke Wutar Lantarkin Maiduguri, Mazauna Suna Fama da Kudin Fetur

Onnoghen: Buhari ya fattakeni ne bayan an ce masa na gana da Atiku a Dubai
Onnoghen: Buhari ya fattakeni ne bayan an ce masa na gana da Atiku a Dubai. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun sheke 'yan bindiga 2, sun cafke masu siyar da makamai a Kaduna

Amma kuma, a yayin kaddamar da wani littafi a Abuja a ranar Juma'a, Onnoghen yace ba a taba fuskantarsa da wani zargi ba kafin a dakatar da shi.

Yace bayan rade-radin cewa ya samu ganawa da Atiku a Dubai, shugaban kasa Buhari bai bashi damar kare kansa ba.

"An yi ta rade-radin cewa na gana da Atiku a Dubai. Amma a yanzu da nake magana, ban taba haduwa ni da Atiku ba a rayuwata. Kamar hakan bai isa ba, an zargeni da sakin manyan 'yan ta'adda. Amma kuma na bar babbar kotu tun a 1978," yace.

A wani labari na daban, Aminu Masari, gwamnan jihar Katsina yace baya goyon bayan yadda Ahmad Gumi, fitaccen malamin addinin Islama ke zuwa domin sasantawa da 'yan bindiga.

Gumi yana kan gaba wurin jan hankalin gwamnati a kan ta sasanta da 'yan bindiga duk da yadda suka tsananta wurin kai hare-hare tare da satar 'yan makaranta.

The Cable ta ruwaito yadda Malamin ke kaiwa 'yan bindiga ziyara a inda suke buya cikin dajikan kasar nan domin kokarin kawo sasanci da kuma shawartarsu da su ajiye makamansu.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel