Dakatar da Onnoghen: Shugaba Buhari yayi wa tsarin mulkin Najeriya karon tsaye - Lauyoyi

Dakatar da Onnoghen: Shugaba Buhari yayi wa tsarin mulkin Najeriya karon tsaye - Lauyoyi

Mun ji cewa wasu manyan Lauyoyin kasar nan sun bayyana cewa taba babban Alkalin Alkalai da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi, ya saba dokar kasa da tsarin mulki, kuma yana iya sa a tsige sa.

Dakatar da Onnoghen: Shugaba Buhari yayi wa tsarin mulkin Najeriya karon tsaye - Lauyoyi
Manyan Lauyoyin Najeriya su na zargin Buhari da saba doka na sauke Onnoghen
Asali: UGC

Mike Ozekhome wanda babban Lauya ne wanda ya kware a harkar dokokin kasa ya bayyana cewa dakatar da Mai shari’a Walter Onnoghen daga matsayin sa na Alkalin Alkalai da shugaba Buhari yayi bai halatta a tsarin mulki ba.

Mike Ozekhome ya bayyana cewa matakin da shugaba Buhari ya dauka haramun ne kuma bai da gindin zama inda yayi kira ga Lauyoyi da su daina shiga kotu. Wasu Lauyoyi da ake ji da su a kasar, sun goyi bayan wannan ra'ayi na Lauyan.

Farfesa Auwalu Yadudu wanda rikakken masani ne a kan harkar shari’a, shi ma ya nuna takaicin sa game da wannan lamari, inda yace shugaban kasar ya shiga cikin abin da ba hurumin sa ba ta hanyar dakatar da babban Alkalin kasar.

KU KARANTA: An hurowa Buhari wuta ya maida tsohon Onnoghen kan kujerar sa

Haka zalika wani babban Lauya kuma Farfesa watau Akiseye George, ya bayyana cewa wannan mataki da shugaban kasar ya dauka, yana iya jawo ‘yan majalisa su tsige sa a doka. Shi ma babban Lauyan ya nemi a rufe duk kotu a kasar.

Abeny Mohammed, wanda shi ma babban Lauya ne wanda yayi kaurin suna a kasar nan ya bayyana cewa sam bai halatta shugaban kasa ya dakatar da babban Alkalin na Najeriya ba ganin yadda yanzu maganar ta ke gaban Kotu.

Daily Trust ta kuma rahoto cewa babban Lauyan nan O.C.J. Okocha, yace dokar kasa ba ta bada hurumi ga shugaban kasa shi kadai ya taba Alkalin Alkalai ba. Sai dai wani Lauya mai suna E.M.D. Umukoro yana ganin ba a saba doka ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng