Bidiyo: Yadda Gwamnan Najeriya Ya Cafke Wasu Ma'aikata Suna Satar Kayan Gwamnati

Bidiyo: Yadda Gwamnan Najeriya Ya Cafke Wasu Ma'aikata Suna Satar Kayan Gwamnati

  • Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru, ya ba da umarnin cafke ma’aikata shida kan karkatar da takardun ma’aikatar lafiya ta jihar
  • An cafke ma'aikatan suna loda takardun da suka haɗa da rajistocin rigakafi da na haihuwa a cikin motoci da niyyar sayar da su
  • Nwifuru ya wallafa bidiyon lokacin da ya cafke ma'aikatan suna aikata wannan danyen aiki, inda aka mika su ga 'yan sanda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ebonyi - Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru, ya bayar da umarnin cafke ma’aikata shida saboda karkatar da wasu takardu daga Ma’aikatar Lafiya ba tare da izini ba.

Ana zargin ma'aikatan sun dade suna sama da fadi da takardun ma'aikatar kamar yadda gwamnan ya ce ya sha ganin ana fitar da takardun a cikin mota.

Gwamnan Ebonyi ya yi ram da wasu ma'aikata da ke satar kayan gwamnati
Gwamnan Ebonyi ya sa an cafke wasu ma'aikata da ya kama suna satar kayan gwamnati. Hoto: @FrancisNwifuru
Asali: Twitter

Gwamna ya cafke barayin kayan gwamnati

Kara karanta wannan

Jigawa: Ma'aikata za su tsunduma yajin aiki kan rashin biyan sabon albashin N70000

A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya nuna yadda aka kama ma’aikatan suna lodin takardu cikin mota da niyyar sace su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Nwifuru ya ce takardun suna da mahimmanci ga cibiyoyin kiwon lafiya da asibitocin jihar amma an shirya siyar da su ba bisa ka’ida ba.

Takardun da aka yi kokarin sace su sun haɗa da katin rigakafi, rajistar haihuwa da rajistar allurar rigafin yara kanana da dai sauransu.

Mai magana da yawunsa, Monday Uzor, ya tabbatar da kama Ndukwe Ayansi da wasu mutum biyar.

An mika masu laifin ga 'yan sanda

An gano cewa ma'aikatan na sayar da kayan ba tare da amincewar gwamnati ba, lamarin da ya sa aka fara bincike.

Bayan cafke su, an ce an mika waɗanda ake zargin ga ‘yan sanda domin bincike da kuma gurfanar da su gaban kuliya manta sabo.

Gwamnan ya yi tir da yunkurin da wasu ke yi na kawo cikas ga ci gaban da ake son kawowa ga jama’ar jihar Ebonyi.

Kara karanta wannan

Gwamna ya umarci cafke wasu ma'aikatan lafiya a jiharsa

Kalli bidiyon a kasa:

Miyagu sun tafka sata a ofishin gwamna

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu bata gari sun fasa ofishin yakin neman zaben gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, suka yashe kayan ciki.

An ce 'yan barayin sun yi amfani da daukewar kafa da dare inda suka yi nasarar fasa ofishin yakin neman zaben na LACO-FSIC tare da satar kayayyaki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.