An Kama Hadimin Gwamna Sule Da Wasu Mutum 16 Kan Satar Kayan Gwamnati

An Kama Hadimin Gwamna Sule Da Wasu Mutum 16 Kan Satar Kayan Gwamnati

- Hukumar ‘yan sandan jihar Nasarawa sun damki mai baiwa gwamnan jihar shawara na musamman da wasu mutane 16

- Kamar yanda kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Bola Longe ya bayyana, ya kamasu da laifun almundahana ne

- A cewarsa, sun baje kolin kwasar kayan aikin titunan jiragen kasa suna sayarwa tare da bushasharsu yadda suka ga dama

Hukumar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta samu nasarar damkar mai baiwa gwamnan jihar, Abdullahi Sule, shawara na musamman da wasu mutane 16 bisa zargin kwasar kayan ayyukan titunan jiragen kasa suna awon gaba dasu a Lafia da karamar hukumar Kaena da ke jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan, CP Bola Longe, ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Lafia, yayin da ya gabatar da wadanda ake zargin a can hedkwatar tsaro, The Punch ta ruwaito.

An Kama Hadimin Gwamna Sule Da Wasu Mutum 16 Kan Satar Kayan Gwamnati
An Kama Hadimin Gwamna Sule Da Wasu Mutum 16 Kan Satar Kayan Gwamnati. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An Kama 'Likitan' Bogi Da Ke Shiga Daji Yana Yi Wa Ƴan Bindiga Aiki a Katsina

Kamar yadda ya bayyana, wadanda ake zargin sun dade da fara harkar kasuwanci da kayan, inda suke kwasa suna sayar dasu yadda sukaga dama har sai da dubunsu ta cika bayan an sanar da hukumar ‘yan sanda wadanda sukayi gaggawar damkarsu.

KU KARANTA: Wata Sabuwa: Farashin Burodi Zai Yi Tashin Gwauron Zabi, Masu Gidajen Burodi Sun Sanar

“Hukumar ta yi amfani da dabara ta musamman ne wurin gano bakin zaren. Abin farincikin shine yadda karshen al’amarin yazo bayan hukumar ‘yan sanda ta rutsa su suna tsaka da cinikayyar kayan titunan jiragen kasa yayin da suke kwasar wasu suna tafiya dasu ta wurin Aguarau Tofa dake karamar hukumar Lafia da Angwan Alago ta Kadarko dake karkashin karamar hukumar Kaena,” a cewarsa.

Bayan wakilin majiyar Legit.ng ya tattauna da mai baiwa gwamnan shawarar, cewa ya yi bai san cewa kayan sata bane kayan da aka sayar masa.

A cewarsa, “Ni dan kasuwa ne. Kuma asalin wanda yake kawomin kaya mutum ne wanda na aminta dashi kawarai. Ya rasu ne watan daya gabata a kan titin Akwanga Nasarawa Eggon sakamakon hatsarin mota. Karon farko kenan da wadannan suka kawomin kaya na siya a hannunsu, kuma na sayar dasu N3,600,000.”

A cikin wadanda ake zargin akwai ‘yan sanda 2, jami’an NSCDC, har da wani dan kasar China guda daya.

A wani labari daban, Ƴan bindiga sun kashe ƴan sa-kai 19 a ƙauyen Yartsakuwa a ƙaramar hukumar Rabah na jihar Sokoto kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin garin, wanda ya yi magana da majiyar Legit.ng a wayar tarho ya ce ƴan sa-kan sun rasa rayukansu ne yayin da suke ƙoƙarin daƙile harin da ƴan bindigan suka kaiwa garin.

Mazaunin garin, da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce yan bindigan sun kai hari ne ƙauyen misalin ƙarfe ɗaya na ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel