Yawan Hare Haren Yan Ta'adda Ya Fusata Gwamna, Zai Yi Garambawul a Bangaren Tsaro
- Yayin da hare-haren yan bindiga ya kara ƙamari a Abia, Gwamna Alex Otti ya shirya rushe tsarin jami'an tsaro a jihar domin shawo kan matsalolin
- Gwamna Otti ya nuna damuwa kan yadda yan bindiga da masu garkuwa suka addabi al'ummar jihar inda ya yi musu gargadi
- Wannan na zuwa ne yayin da a cikin yan kwanakin nan yan ta'adda suka addabi jihar har da kisan jami'an tsaro da dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Abia - Gwamna Alex Otto na jihar Abia ya shirya yin garambawul a bangaren tsaron jihar.
Gwamna Otti ya ce ya yanke shawarar yin hakan ne yayin da jihar ke fama da yawan hare-haren yan bindiga.
Gwamna zai yi garambawul a bangaren tsaro
Otti ya bayyana haka ne yayin hira da yan jaridu bayan ganawa da kwamitin tsaro yayin da ake fama da yan ta'adda, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Otti ya ce ya ji dadi yadda kwamitin suka yi zama tare da yanke shawarar yin sauye-sauye a bangaren tsaro.
"Dukanmu mun zauna mun yi duba zuwa ga tsare-tsaren tsari a Abia, ina murna dukanmu mun amince za mu yi garambawul."
"Mun yi hakan ne domin tabbatar da hare-haren yan bindiga ya zama tarihi, kuma mun yi alkawarin zakulo dukan masu laifuffuka a duk inda suka buya."
- Alex Otti
Gwamna ya yi gargadin karshe ga yan bindiga
Gwamna Otti ya kuma yi zazzafan gargadi ga yan ta'adda da masu aikata laifuffuka cewa jihar ba wurin zamansu ba ne, Tribune ta ruwaito.
Gwamnan ya ba yan ta'adda sanarwa ta musamman inda ya ce idan ka san kai dan ta'adda ne ko mai garkuwa Abia ba wurin zama ba ne.
Gwamna ya gano masu ingiza ta'addanci
Kun ji cewa Gwamna Alex Otti ya yi ikirarin cewa gwamnatinsa ta gano wasu ƴan siyasa da ke ɗaukar nauyin hare-haren ƴan bindiga a Abia.
Otti ya ce bayanan da aka tattara daga nutane da wasu majiyoyi sun nuna babu hannun ƙungiyar ƴan aware IPOB a matsalar tsaron jihar.
Ya ce gwamnatinsa ba za ta ɗaga wa kowa kafa ba, za ta sa kafar wando ɗaya da duk mai hannu a hare-haren ƴan bindiga.
Asali: Legit.ng