Gwamna Ya Rushe Sababbin Masarautu da Tsohon Gwamna Ya Samar, Ya daga Kimar Sarki

Gwamna Ya Rushe Sababbin Masarautu da Tsohon Gwamna Ya Samar, Ya daga Kimar Sarki

  • Gwamnatin jihar Edo ta dauki wasu muhimman matakai kan sababbin masarautu da wata cibiyar al'adu
  • Gwamna Monday Okpebholo shi ya dauki matakin inda ya dawowa Oba na Benin, Oba Ewuare II martabarsa
  • Wannan na zuwa ne bayan kirkirar sababbin masarautu da tsohuwar gwamnatin Godwin Obaseki ta yi a zamaninta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Gwamna Monday Okpebholo ya rusa dokar masarautu da tsohuwar gwamnatin Godwin Obaseki ta kirkira.

Gwamna Okpebholo ya rusa masarautun ne inda ya dawo da ainihin ikon Oba na Benin, Oba Ewuare II a jihar bayan rage masa kima a baya.

Gwamna ya rushe sababbin masarautu da gwamnatin baya ta kirkira
Gwamna Monday Okpebholo ya dawowa da Oba na Benin martabarsa a jihar Edo. Hoto: Sen. Monday Okpebholo.
Asali: Twitter

Gwamna ya rushe sababbin masarautu a Edo

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran Gwamna Okpebholo, Fred Itua ya fitar, cewar Punch.

Kara karanta wannan

An zo wurin: Gwamna ya gaza hakuri, ya kafa kwamitin binciken tsohon gwamnan jiharsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dawo da martabar Oba Ewuare II shi ke tabbatar da rusa dokar masarauta a Edo ta Kudu da Godwin Obaseki ya kirkira a lokacin mulkinsa.

Sanarwar ta ce gwamnan ya kuma ki amincewa da kwace cibiyar al'adu ta Oba Akenzua II da tsohuwar gwamnatin ta yi, Channels TV ta ruwaito.

"Wannan gwamnatin ta dawo da cibiyar al'adu ta Oba Akenzua domin gudanar da abin aikin da aka kirkire ta dominsa."
"Gwamnatin kuma ta rushe sababbin masarautu da tsohuwar gwamnatin Obaseki ta kirkira a yankin Edo ta Kudu."

- Cewar sanarwar

Gwamna ya bayyana goyon bayansa ga sarakuna

Gwamna Okpebholo ya bayyana himmatuwarsa wurin tabbatar da ba sarakunan gargajiya goyon baya na musamman a jihar yayin sake neman hadin kansu a halin yanzu.

Okpebholo ya kuma yi alkawarin ba Oba na Benin dukan gudunmawa da yake bukata domin cigaba da taka rawa a bangaren gargajiya.

Gwamna Okpebholo zai binciki gwamnatin Obaseki

Kara karanta wannan

Ba a gama da zargin rigima tsakaninsu ba, Kanin Kwankwaso ya maka Abba a kotu

Kun ji cewa Gwamna Monday Okpebholo na Edo ya kafa kwamitin fara binciken tsohuwar gwamnatin jihar da ta sauka.

Okpebholo ya kafa kwamitin ne mai dauke da mutane 14 domin binciken tsohon Gwamna, Godwin Obaseki bayan barin mulki.

Wannan na zuwa ne kwanaki 12 bayan an rantsar da Okpebholo a matsayin gwamnan jihar bayan nasara a zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.